Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Mallam Garba Shehu, ya bayyana dalilin da Shugaba Muhammadu Buhari bai mika wa mataimakinsa ragamar jagorancin kasar ba yayin tafiyarsa birnin Landan ganin likita.
Yayin wani shiri na siyasa da gidan Talabijin na Channels ya shirya a Yammacin ranar Talata, Mallam Garba ya ce kwanakin da Shugaban kasar zai dauka a wajen Najeriya kalilan ne da ba su kai ga ya mika wa Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo akalar jagorancin kasar ba.
- Bikin ranar haihuwar Tinubu ya bar baya da kura
- Majalisar Musulunci ta yi wa CAN tatas kan nadin alkalai
Hadimin Shugaban Kasar ya ce ubangidansa bai karya wata doka ba don zai ci gaba da aiki daga duk inda ya kasance.
A cewarsa, “abin da doka ta tanada shi ne idan Shugaban Kasa zai kai kwana 21 ko fiye, to ya wajaba ya mika wa mataimakinsa mulki, amma a irin wannan yanayi bai kasance dole ba.”
A safiyar Talatar da ta gabata ce Shugaba Buhari ya tafi kasar Birtaniya domin a duba lafiyarsa kamar yadda aka saba.
Sanarwar da Fadar Shugaban Kasar ta fitar ta ce ana sa ran zai dawo Najeriya a mako na biyu na watan Afrilu.
Tafiyar da shugaban kasar ya yi ita ce karon farko da ya fita ketare tun bayan bullar annobar Coronavirus.
A shekarar 2017 ne shugaban ya shafe kwanaki 103 yana jinya a Landan, mataimakinsa ne ya zama mukaddashin Shugaban Kasa.