Hausawa a wurare irin su Jamhuriyar Nijar, Arewacin Najeriya, Sudan, Gana da wasu ƙasashe na da wata dabi’a da aka san su da ita ta sanya wa ‘ya’yansu sunayen annabawa da alayensu, sannan sai nasu na gargajiya na musamman da ke biye musu a matsayin suna na biyu ko na uku. Irin wannan sunayen na gargajiya sun fi ƙamari ne ga Hausawan da ke cikin ƙauyuka ko kananan garuruwa, in aka keɓe takwarorinsu na birane, inda wasu ke kallon haka a rashin wayewa sukutum. Ba su san cewa da yawa daga sunayen da suke ɗauka cewa na Larabawa ne, ba na Larabawan ba ne a asali. Sunaye irinsu Nuhu (Noah), Ibrahim (Abraham), Dawud, Dauda (Dabid), Idris (Enoch), Imran, Isah, Shammil (Samuel), Hana (Hannah), Yunusa (Jonah) da sauransu ba sunayen Larabawa ba ne kuma ba su da ma’ana a harshen Larabci. Larabawa na misalta sunayen da cewa sunan Annabin Allah wane, amman a harshen Hausa, da yawa na da ma’ana, kasancewar Hausa na daga cikin daɗaɗɗun alƙaryoyin Afrika da suka yi zamani a Yankin Gabas ta tsakiya a daure ta bakin manazarta harshen hausa.
Sunayen Hausawa na gargajiya ana sanya wa yara sabbin haihuwa ko manya bayan sun girma, dangane da yanayin haihuwarsu, jerin yaran a cikin daki da matsayin mutane a gari bayan sun manyanta. A gargajiyar Bahaushe, ana ambaton waɗannan sunaye da “sunayen kakanni” waɗanda su ne jigogi a kowane gidan. Duk mai jin Hausa na iya gane ma’anar sunayen saboda zurfafan kalaman Hausa da ke tattare da su da dabi’arsu da ke tattare a cikin sunayen. Kuma har wa yau gungun kabilun Hausawa daban-daban na amfani da sunayen irin su; Gobirawa, Tagamawa, Adarawa, Kurfayawa, Cidarawa, Arawa, Daurawa, Kanawa, Kabawa, Katsinawa, Ranawa, Hadejawa, Zazzagawa, Zamfarawa da sauransu.
Su kuma waɗanda suke zaman jakadun gidansu, ƙauyukansu, garuruwansu da jihohinsu na sa sunan cikin sunansu na za ne kamar Bashir Adamu Gobir, Abubakar Ibrahim Gobir, Aminu Yahaya Sakkwato, Nuhu Gobir, Alhaji Adam Rano, Bashir Abubakar Katsina, Malam Kabiru Daura,
Sunayen Hausawa na gargajiya na maza:
Bizo: Wannan suna ana sa ma ɗa namiji shi wanda aka haifa a ɗaki bayan magajinnai nai na rasuwa. Kamar yadda gargajiyar dake tareda wannan sunan ta bafada, yaron da aka haifa a cikin wannan yanayi ana ɗaukar sa a kai shi bisa bilbizo a ba iskoki hakuri kuma ana dacewa da sa’a yaron su ya rayu, wanda shine dalilin da yasa ake kiran su da suna “Bizo”, kalmar hausa dake nufin wurin da ake zubar da shara. Su kuma wanda ba’a kaisu bizo ba ana kiransu “Barau”, bayan cewar “A barshi a gani ko ya tsaya’ rayu’.”
Dawo, Dandawo: Da namiji wanda aka haifa lokacin da uwarsa ke kirɓin dawo, abinci dangin gero da ake haɗawa tare da nono a samu hura.
Arzika: Ɗa namiji wanda uwarsa ta sha wahalar nakuda ga haihuwarsa kafin daga bisani aka haife shi.
Dawi, Maidawa: Ɗa namiji wanda aka haifa a lokacin da babansa ya girbe dawa da yawa.
Gerau, Maigero: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacin da babansa ya girbe damman hatsi da yawa.
Maiwake: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacinda babansa ya girbe wake da yawa.
Shekarau: Ɗa namiji wanda uwarsa ta ɗauki cikinsa tsawon shekara guda.
Ruwa, Anaruwa,
Makau: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacin da ake shata ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a cikin gari.
Hankurau: Namiji wanda yake da yawancin hakuri da mutane a gari.
Shukau: Namiji wanda aka haifa lokacin da ake shuka.
Nomau: Namiji wanda aka haifa lokacin da ake noma.
Sarki: Ɗa mai sunan sarki. Namiji wanda ke da sunan sarki a masarauta.
Maifari: Namiji wanda aka haifa lokacin fari.
Nagona, Nanoma: Namiji wanda aka haifa a gona.
Bako: Namiji wanda aka haifa lokacin da aka yi baƙi a cikin gida
Bara: Ɗa namiji na farko da aka haifa bayan an haifi mata. Bara a Hausa na nufin roko ke nan, wato roko shi suka yi.
Hana: Namiji wanda aka haifa a cikin gida lokacin da suke zaman makokin mutuwar dan gida ko yar gida.
Bawa: Namiji wanda ya girma wajen wata macce wadda ba uwarsa ba.
Tunau: Ana iya cewa “Tuni” ma’ana tunowa da haihuwa. Namiji wanda aka haifa bayan uwar shi ta ɗauki tsawon lokacin kafin ta sake ɗaukar ciki.
Maikasuwa: Ɗan kasuwa ko mai kasuwa.
Kasu, kasuwa: Ɗa namiji wanda aka haifa a kasuwa ko ranar kasuwa a gari.
Tanko: Ɗa namiji kanen mata a cikin ɗaki.
Abara, Abarshi,
Barau: Ɗa namiji da ya rage bayan magajinnai nai na rasuwa.
Dangali: Ɗa namiji guda ɗaya tilo da aka haifa a ɗaki
Jika: Jikan wani. Namiji wanda yakeda sunan jikan wani.
Babba: Magajin wani ko wa. Namiji wanda yake da sunan magajin wani.
Kane: Karamin kanen wani. Namiji wanda yake da sunan kanen wani.
Maikudi: Wanda yake da kuɗi ko dukiya.
Madugu: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacin tafiya ko wanda aka haifa cikin yanayin tafiya.
Kaka: Mai sunan kakanni. Wanda yakeda sunan kakan wani.
Tagwaye: ‘Yan biyu ke nan.
Gambo: kanen ‘yan tagwaye.
Kokari: Mutum wanda yake da yawancin kokari a gari.
Adare: Ɗa namiji wanda aka haifa da dare.
Fari ko Hwari, Jatau: Namiji wanda yake da fari kamar madara.
Baki, Duna: Namiji wanda yake da baki wuluk.
Nahantsi ko hantsi: Namiji wanda aka haifa da hantsi.
Agada: Sa-maza-sa-mata. Namiji ko macce wadda take bi ma tagwaye.
Dada: Ɗa namiji wanda uwarsa da babansa dangin juna ne.
Kulau: Namiji wanda aka fi so a ɗakinsu.
Nagoma: Ɗa namiji wanda yake cikon na goma a ɗakinsu.
Bakwai: Ɗa namiji wanda yake cikon na bakwai a ɗakinsu.
Auta: Yaro na karshe a ɗakinsa.
Jigo: Shugaba. Ɗa namiji wanda aka haifa cikin mata, ke nan ya zamo shugabansu.
Karami: Mai karamin jiki ko karamin ka nen wani.
Guntau: Guntun mutum.
Jariri: Ɗa namiji wanda yake da karantar gaske lokacin haihuwa.
Ango: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacin da ake shagalin aure a cikin gidansu.
Korau: Ɗa namiji wanda aka haifa lokacin da aka saki uwarsa.
Ɗari: Wanda aka haifa lokacin da ake matsanancin sanyi.
Kadaɗe: Ɗa namiji wanda aka haifa bayan bayan iyayensa sun daɗe ba su taɓa haihuwa ba kafin daga bisani a haife shi.
Babangida: Ana sa wa yaro wannan sunan in yana da suna guda da kakansa a gida kuma saboda surukai suna jin kunyar faɗin sunan sak, sai su laƙaba masa “Babangida”, wato babban cikin gida.
Mun dauko wannan rubutun daga intanet wanda dan Zubairu ya makalashi