Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC) ta tabbatar da cewa wasu da da ta kai ga sanin ko su wane ne ba sun yi kutse a shafinta na intanet a karshen makon jiya.
Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya tabbatar da haka, amma ya ce an yi nasarar magance matsalar a kan kari.
- Zanga-zangar #EndSARS ta kassara Tattalin Arzikin Kasa —Minista
- Kotu ta ba Ndume kwana 21 ya nemo Maina
“Duk da cewa an yi kokarin yi wa shafin mu kutse a karshen makon jiya, an dakile harin kuma yanzu shafin na aiki yadda ya kamata”, inji wani sako da ya wallafa ta Twitter.
Idan ba a manta ba a ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu da masu fafutkika masu taken ‘Babu wanda ya san mu’, a cikin wasu jerin sakonnin da suka fitar ta intanet suka ce sun yi kutse a shafukan wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya domin goyon bayan masu zanga-zangar #EndSARS da ke gudana a kasar.
Hukumomin da suka ce sun yi wa kutse su ne EFCC, Babban Bankin Najeriya (CBN), Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da sauransu.
A lokacin da wakilinmu ya yi kokarin shiga shafin EFCC a ranar Juma’a sai ya samu sakon cewa shafin na da matsala.
Idan ba a manta ba maharan sun yi kutse a shafin Twitter na Hukumar Kula da Kafafen Watsa Labarai, inda suka wallafa sakon goyon bayan zanga-zangar #EndSARS.