Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya ce tabbas akwai wasu ’ya’yan Jam’iyyar APC da ke yi wa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar aiki don kada Tinubu.
Tsohon ministan ya bayyana hakan ne a gidan talabijin na Channels, a ranar Laraba.
- NAJERIYA A YAU: Wa Ke Yi Wa Tinubu Kafar Ungulu?
- Wike ya hana Atiku wurin taron yakin neman zabe a Ribas
“Duk wadannan abubuwan da ke faruwa na da matukar tayar da hankali domin muna aiki tukuru amma wasu na aiki dare da rana don kawo cikas a kan tafiyarmu ba su so mu kai ga nasara.
“A tunanina wasu na yin hakan ne amma ba za su yi nasara ba, saboda jam’iyyar adawa ba ta da wani karfi amma tabbas akwai wadanda suke yi wa Atiku aiki,” in ji Fani-Kayode.
Ya kuma mayar da martani kan ikirarin da Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi na cewa akwai wasu a fadar shugaban kasa da ke neman yi wa takarar Tinubu kafar ungulu a zabe mai zuwa.
Ya ce dalilin da ya sa hakan ke faruwa a halin yanzu, shi ne don suna so su fusata kowa sannan ta bare da jam’iyyar baki daya.
Sai dai Fani Kayode ya ce duk da manakisar da ake shirya wa Tinubu, zai kai ga nasara idan ya lashe zaben shugaban kasa