✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Tabarbarewar Ilimi: Gwamnonin Kudu maso Yamma sun sauka daga tafarkin Awolowo —NNPP

Idan Kwankwaso ya lashe zabe zai dawo da Najeriya kan tafarki madaidaici.

Jam’iyyar NNPP ta zargi Gwamnonin Kudu maso Yamma da sauka daga tafarkin da tsohon Shugaban Kasa Obafemi Awolowo ya dora bangaren ilimin yankin a kai.

Sakataren Jam’iyyar na kasa, Dipo Olayokun ne ya bayyana hakan a Abekuta, babban birnin Jihar Ogun, yayin kaddamar da kungiyoyin yakin neman zaben dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar, Sanata Rabiu Kwankwaso a yankin.

Olayokun ya kuma zargi Gwamnonin da kirkirar sabbin tsare-tsare marasa amfani, wadanda ba su haifar wa ilimin yankin komai ba sai durkushewa.

“Muna fama da matsalar malamai marasa inganci, tsare-stare marasa amfani, da sauran tarin matsaloli da suka lalata mana ilimin makarantun gwamnati.

“A da, daidai da kasa baki daya na alfahari da yankinmu, amma gwamnoninmu yanzu duk sun lalata tsarin da Awolowo ya dora mu a kai,” in ji shi.

A nasa bangaren Shugaba Kungiyar Yakin Neman Zaben Kwankwaso, Wasiu Ajirotuntun, ya ce da zarar dan takarar ta su ya samu nasarar darewa karagar shugabancin kasar, zai dawo da Najeriya kan tafarki madaidaici.