Masu iya magana na cewa mutuwa ba ruwanki da sabo. Tabbas wannan magana haka take, amma ba za ka san da hakan ba, sai lokacin da mutuwa ta dauke wani na kusa da kai. Babu shakka na kasance daga cikin wadanda suka san zafin mutuwa, bayan da na wayi gari na tashi da labarin rasuwar aminina Furodusa Ibrahim B. Nuhu a safiyar ranar Talata 11 ga watan Yuni, 2013. Allah Ya yi masa rahama da ma duk wani Musulmi da ya riga mu gidan gaskiya.
Idan na ce zan waiwayi irin zaman da na yi da marigayin, wannan shafi ba zai iya dauke kyawawan halayensa da zan zayyano ba, saboda na jima da saninsa tun a lokacin da na fara ganinsa a fim din Gambiza har zuwa lokacin rasuwarsa ba mu taba samun sabani ba. Mun shaku sosai.
A iya zaman da na yi da shi ban taba ganin an yi rigima da shi a lokeshin ba, domin yakan nesanta kansa daga cikin al’amuran da ba su shafe shi ba. Marigayin na da saukin kai, yana da biyayya da girmama na gaba da shi, wanda hakan ne ya sa ya samu gindin zama a gurin ubangidansa Ali Nuhu. Marigayin ya dauki Ali tamkar uba kasancewar a gidansa yake zama.
Dalilin shakuwar da na yi da shi har ya ba ni tarihin yadda aka yi suka hadu da Ali Nuhu da kuma yadda iyayensa suka damka amanarsa ga Alin, wanda a dalilin amanarsa da Alin ya rike ne har wasu suke ganin tamkar dan uwansa ne na jini.
Marigayi Ibrahim dai ba za mu sake ganinsa ba har sai lokacin da Allah Zai hada fuskokin a ranar gobe kiyama, wanda muke fatan Allah Ya hada mu tare a inuwar Annabi (S.A.W) da sauran duk wani Musulmi baki daya.
Ka rabu da mu, amma har gobe kana nan cikin zuciyarmu saboda irin zaman amanar da muka yi da kai, don haka duk lokacin da muka tuna ka, za mu yi maka addu’a.
Aliyu Ahmad dan jarida ne, ya rubuto daga garin Mararraba, wadda ke iyakar Abuja da Jihar Nassarawa, 07069139120.
Ta’azziyar Ibrahim B. Nuhu: Furodusa mai saukin kai
Masu iya magana na cewa mutuwa ba ruwanki da sabo. Tabbas wannan magana haka take, amma ba za ka san da hakan ba, sai lokacin…