A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka yi jana’izar fitaccen zakaran damben duniya Muhammad Ali, wanda shi ne mashawurin dan wasan motsa jiki na karni na 20, an binne shi ne a garinsu wato Louisbille a Kentucky da ke kasar Amurka. dan wasan wanda ya samu kambun zakaran damben na duniya ajin masu nauyi, ya rasu ne a ranar 3 ga watan Mayu, yana da shekara 74. Rasuwarsa wani babban rashi ne da duniya ta yi wanda da wuya a samu madadinsa a lokaci mai tsawo.
dan wasan wanda mahaifiyansa ya sanya wa sunan Cassius Marcellus Clay (Junior), ya sauya sunansa daga ‘sunan da ya kira sunan bayi’ zuwa Muhammad Ali a ranar 6 ga watan Maris din shekarar 1964.
Ali ya zama wani mashawurin dan dambe a shekarun 1960, inda yake amfani da karfi da basira da salo da kuma dabaru iri-iri, wadanda suka sa aka sanya masa lakabin ‘The Louisbille Lip’ wato kyauren Louisbille.
A wajen filin wasa, Ali ya kasance wani mutum ne mai kaifin hankali. A shekarar 1966 ya ki amincewa a sanya sunansa a cikin dakarun Amurka da za su je yakin bietnam, inda ya ce sojojin bietnam ba su aikata laifin da Amurkawa fararen fata suke yi na nuna wariya ba. Ya ce yana adawa da yakin da kasarsa ta shiga musamman saboda kasancewarsa Minista a wata kungiyar addinin Musulunci ta Amurkawa Bakaken Fata, mai suna Nation of Islam. Sai dai saboda matsayinsa game da yakin, Hukumar da ke Sanya Ido a kan Harkokin Wasannin kasar Amurka ta kwace duka lambobin girmamawan da ya samu. Bayan kwana 10 kuma, wani kwamitin bincike da aka kafa ya same shi da laifi kuma ya ba da umarni a daure shi shekara biyar a gidan yari da cinsa tarar Dala dubu 10. Saboda haka dan wasan bai iya yin wasa ba har tsawon shekara hudu, amma lokacin da ya daukaka kara zuwa Kotun kolin Amurka, kotun ta ba da umarnin dakatar da tsare shi a shekarar 1971.
Daga nan ne Ali ya dawo wasa, kodayake kokarinsa na kare kambunsa daga Joe Frazier ya ci tura, amma ya kama hanyar zama zakaran damben duniya. Ya samu dimbin nasarori daga abokan karawarsa, wadanda suka sanya a shekarar 1974 ya zama zakaran damben duniya a ajin masu nauyi bayan ya kashe George Foreman. Wasan wanda aka yi masa take da “Rumble in the Jungle” wato Karon Batar karfe wanda aka yi birnin Kinshasa a tsohuwar kasar Zaire, shi ne babban wasan Ali da ba za a iya mantawa da shi ba.
Bayan shekara 10, Ali ya kara samun nasarar zama zakaran damben duniya ajin masu nauyi har sau biyu. Shi ne mutum guda da ya taba samun lambar har sau uku a tarihi. kokarinsa na samun lambar a karo na hudu ya gamu da cikas, bayan da ya yi rashin nasara. Daga nan ne sai ya yi ritaya daga wasa. Ko bayan da ya yi ritaya, an ci gaba da damawa da shiga a al’amuran duniya kuma duniya ta ba shi matsayin jakadan wanzar da zaman lafiya.
Bayan wasan dambe, Muhammad Ali wani jigo ne a kungiyar kare hakkin Amurkawa. Yana alfahari da yadda ake danganta shi da asalinsa na bakaken fata, kuma ya tsani nuna wariyar launin fata, ba ya sassautawa wajen sukar wariyar launin fata. Har ila yau, Ali ya dauki addininsa na Musulunci da muhimmanci matuka. Ya fara ne da shiga kungiyar Nation of Islam karkashin jagorancin Elijah Mohammed, amma daga bisani da Ali ya hadu da masu tsananin kishin Islama, ya karbi akidar Sunni.
Ana kaunar Muhammad Ali a duk fadin nahiyar Afirka da ma duniya baki daya. Kodayake, akwai wani lokaci guda da aikinsa ya ci karo da muradun nahiyar Afirka, wato a shekarar 1980 lokacin da Shugaban Amurka Jimmy Carter ya tura shi nahiyar don ya yi kira ga kaurace wa wasannin Olympics din Bazara da za a yi a birnin Moscow na kasar Rasha. Sai dai ’yan Afirka sun yi watsi da bukatarsa saboda kasashen Yammacin Duniya sun taba yin watsi da irin wannan kiran da nahiyar ta taba yi na cewa a kauracewa wasannin Olympics din birnin Montreal na kasar Kanada a shekarar 1976 saboda yadda kasar New Zealand take goyon bayan gwamnatin wariyar launin fata da take mulki a kasar Afirka ta Kudu a lokacin.
Ali wani Bakin Ba’amurke ne da ya samu daukaka, inda ya zama babban zakaran damben duniya, kuma ya samu daukaka wadda ta yi kusa da ta marigayi Nelson Mandela.
Ali ya rasu ne bayan ya kwashe shekaru masu yawa yana fama da cutar Parkinson (cutar karmar sassan jiki), ya bayyana kamu da cutar ne ga duniya a shekarar 1984. Rayuwarsa tana kunshe da darussa kyawawa wadanda za su amfani bakaken fata da ma duniya baki daya.
A gaskiya, Ali wani babban gwarzo ne. Allah Ya jikansa da rahma.
Ta’aziyyar Muhammad Ali 01
A ranar Juma’ar da ta gabata ne aka yi jana’izar fitaccen zakaran damben duniya Muhammad Ali, wanda shi ne mashawurin dan wasan motsa jiki na…