Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta dage shari’ar da ake yi wa shugaban kungiyar ‘yan awaren Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu bisa zargin ta’addanci har sai abin da hali ya yi.
Mai Shari’a Binta Nyako ta ce an dage shari’ar ce saboda karar da Gwamnatin Tarayya ta shigar kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke kan Kanu a ranar 13 ga watan Oktoba, wadda ta wanke shi daga zarge-zargen alaka da ta’addanci.
- ’Yan ta’adda 19 da sojoji ke nema ruwa a jallo
- Tashin bam a Istanbul: ‘Yan sandan Turkiyya sun kama mutum 46
Wannan dai na zuwa ne yayin da aka ce jagoran kungiyar ’yan awaren ya ki bayyana a gaban kotu domin yi masa shari’a kan rashin nuna amincewa da matakin Gwamnatin Tarayya na kin bin umarnin Kotun Daukaka Kara.
Lauyan da ya shigar da kara, Mohammed Abubakar, ya sanar da alkalin da ke shari’ar Kanu na kin halartar zaman shari’ar, inda ya bayyana cewa ya yi hakan ne saboda abin da ya kira rashin adalci.
Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ne ya shigar da karar, inda ya kalubalanci hukuncin da aka yanke wa Kanu kan tuhume-tuhume 15 da ake masa wanda suka shafi ta’addanci da cin amanar kasa.
Kotun Daukaka Kara ta yanke hukuncin cewa Babbar Kotun Tarayya da ke sauraron shari’ar ba ta da hurumi a kan hakan.