✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’addanci: Kashe-kashen ya isa haka nan

Ga duk wanda ya kwana ya tashi a kasar nan, al’amarin nan yana ba shi takaici – kullum sai kashe bayin Allah ake a kasar…

Ga duk wanda ya kwana ya tashi a kasar nan, al’amarin nan yana ba shi takaici – kullum sai kashe bayin Allah ake a kasar nan, musamman ma Arewa, sai lalata dukiya ake, ga shi kuma ana ci gaba da cin zarafin ’ya’ya mata. Domin gargadi da nuna alhininsa, Malam Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi Tashar Gusau (08069807496) ya rubuto wannan tsokaci:
Ko shakka babu zara ba ta barin dame. A yau ina magana ne a kan kashe-kashen gillar da ake ci gaba da yi wa ’yan uwa ’yan Arewa a kowace safiyar Allah ta’ala. Wanda ko shakka babu ya kamata al’ummar Arewa mu tashi tsaye mu yaki wannan matsalar tun kafin wankin hula ya iyar da kai mu dare.
Domin idan muka yi la’akari, a duk safiyar Allah ana ci gaba da lahanta al’ummarmu ne, wanda tun ana kashe mu lokaci zuwa lokaci; to yau an wayi gari kusan kullum sai an kashe daruruwan al’ummarmu, ba a biranenmu kadai abin ya tsaya ba har kauyukanmu abin ya shafa. Kuma abin ba a boye yake ba, kowa ya san a can tali-tali, wasu daidaikun garuruwa ne kadai abin ya shafa amma yanzu kusan kowane lungu da sako na Arewa ya shafa.
Don haka ya zama dolen dole mu farka daga wannan mummunan barcin da ke kokarin nakasar da mu. In ba haka ba, wallahi sannu a hankali za a wayi gari al’ummar Arewa sun zama turbaya, sai dai kokarin shiga ba da tarihin samuwarmu a doron kasa kamar yadda ake bayar da tarihin Samudawa da Adawa ba.
Daga karshe nake rokon Allah Ya daukaki Arewa da al’ummar Arewa. Allah Ka tona asirin masu alhakin wannan aika-aikar. Ya Allah Ka wargaza masu kokarin wargaza wannan yanki namu. Ya Allah Ka isar mana da isarKa. Ya Allah Ka sa reshe ya juye da mujiya. Allahumma amin!