Ta yiwu Jam’iyyar APC ta gudanar da babban taronta a birnin Ikko na jihar Legas.
Wata majiya a jam’iyyar ta fada wa Aminiya jiya cewa babban taron zai gudana a Legas duk da korafin da wasu manya masu ruwa da tsaki suka nuna na tsoron yiwuwar rashin kare muradunsu idan aka yi taron a wajen garin Abuja.
“A Legas za a yi babban taron duk da da dardar din da wasu ’yan jam’iyyar suke yi. An amince da haka kuma ana sanya ido ga wadanda za su yi murdiya”. Majiyar ta ce.
A ranar Lahadin da ta gabata, shugabannin jam’iyyar sun fitar da membobin kwamitin babban taron su 68 karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Badaru.
A wata sanarwar da Sakataren Shirye-Shirye na jam’iyyar APC yasanya wa hannu ta nuna cewa Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo shi ne mataimakin shugaban kwamitin sai Sanata Ben Uwajumogu a matsayin sakatare kuma memba na kwamitin.