✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ta yi taron majalisar ’yan agajinta a Gombe

Majalisar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta gudanar da taronta na kasa a Jihar Gombe inda ta tattauna matsalolin da suka…

Majalisar agaji ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta gudanar da taronta na kasa a Jihar Gombe inda ta tattauna matsalolin da suka shafi kyautatuwarta.
Da yake wa manema labarai karin haske kan makasudin taron, Babban Darakta na kasa, Injiniya Mustapha Imam Sitti, ya ce ana gudanar da shi ne don shawo kan matsalolin da suka shafi kungiya da kuma irin ayyukan da za a fuskanta a gaba. Kuma akan fadakar da ’yan agaji dabarun kula da marasa lafiya idan sun kai dauki  da kuma yadda za a ba da agajin gaggawa a duk lokacin da bukatar haka ta taso.
A cewarsa, akan duba irin nasarorin da suka samu a shekarar da ta gabata, sannan a bullo da irin tsare-tsaren da suka kamata a fuskanta.
Daraktan ya ce sukan gudanar da irin wannan taro sau uku ko sau hudu a kowace shekara, sannan kuma su yi na kara wa juna sani don kara inganta ayyukan mambobin  kungiyar  ta yadda za su sami kyakkyawar makama.
Darakta Mustapha ya ce daya daga cikin muhimman nasarori da suka samu ita ce mutane suna fahimtar aikin da suke yi, kuma suna natsuwa da su. Ya yi nunin ba a Najeriya kadai kungiyar take aiki ba, a’a, hatta a kasashe irin su Saudi Arebiya da Benin da Ghana da Kamaru.
Injiniya Mustapha Sitti, ya nuna takaicinsa na rashin samun tallafi a lokacin da ya kamata, musamman ma a sassan da suke da muhimmancin da ya kamata a ce sun bayar da agaji, shi ya sa ma ya bayyana cewa babban burin kungiyar shi ne ta kara fadada ayyukanta ta kowace hanya don taimakon al’umma.
Yayin da yake tsokaci, shugaban kungiyar Izala na jihar ta Gombe, wanda kuma shi ne babban sakataren tsare-tsare na kungiyar ’yan agaji ta kasa, Alhaji Salisu Muhammad Gombe, gode wa shugabannin kungiyar ya yi kan yadda suka zabi jihar don gudanar da wannan taro.