✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta yi iƙirarin rashin ci da sha a sama da shekara 16

Matashiyar ta yi gwajin lafiya da yawa a ƙasar Habasha, sai dai babu wanda zai iya tabbatar da gaskiyar abin da ta faɗa.

Wata mai suna Muluwork Ambaw, ’yar ƙasar Habasha mai shekara 26, ta yi iƙirarin  cewa ta shafe shekara 16 a  rayuwarta ba tare da ci ko sha ba.

Da ƙyar mutane ke iya wuce sa’o’i masu yawa ba tare da sun ci wani abu ba, amma Muluwork Ambaw ta ce ta ƙaurace wa abinci tun lokacin da take da shekara 10, bayan da ta daina sha’awar cin abinci.

Baya ga rashin wadataccen abincin da take fama da shi, rahotanni sun nuna Muluwork tana cikin ƙoshin lafiya kuma tana da kuzarin da za ta iya gudanar da ayyukanta na yau da kullum da suka haɗa da dafa abinci ga wasu da gudanar da ayyuka daban-daban.

Matashiyar ta yi gwajin lafiya da yawa a ƙasar Habasha, sai dai babu wanda zai iya tabbatar da gaskiyar abin da ta faɗa, duk da cewa likitocin wani asibiti a birnin Addis Ababa sun tabbatar da cewa babu wani abinci a cikin hanjinta a lokacin da ake gwajin.

Batun Muluwork Ambaw ya yaɗu bayan wani mai suna Drew Binsky ya ziyarce ta wanda ya ji labarinta yayin da ya ziyarci Habasha kuma ya yanke shawarar ganawa da ita.

Bidiyonsa ya yi saurin yaɗuwa, amma ba wannan ne karo na farko da labarin Muluwork ya ja hanakalin jama’a a kafofin yaɗa labarai ba.

Ta fara jan hankali ne a shekarar 2016, lokacin da aka yaɗa jita-jita game da yarinyar da za ta iya rayuwa ba tare da abinci ko ruwa ba a ƙasar.

’Yan jarida da masu ba da rahoto a talabijin sun taru a ƙaramin ƙauyenta don tattara labarinta mai ban-mamaki.

Mai shekara 26 ta ce, har yanzu ba za ta iya tuna lokacin da abinci ya wuce ta leɓenta ba.

Abincinta na ƙarshe shi ne abincin ƙasar mai suna lentil stew da injera, kuma ta ce bayan ta gama cin abincin ne sai kawai buƙatar abincin ta gushe mata.

Da farko tana yi wa danginta ƙaryar cewa tana ci, amma daga baya ta gaya musu gaskiya.

“Na kasance tare da iyalina, kuma sun ce in ci karin kumallo in tafi makaranta,” Muluwork ta tuna. “Na ce na ci abinci amma gaskiyar lamari ban ci ba. Na rasa sha’awar shan ruwa ko cin abinci.”

Matashiyar ’yar Habasha ta yi iƙirarin cewa saboda ba ta ci abinci ko shan ruwa ba a cikin shekara 16, hakan ya sa ba ta amfani da ban-ɗaki a tsawon lokacin, in ba dai za ta yi wanka ba.

A shekarar 2021, shafin labarai na Habasha Borkena ya ce Firayi Ministan ƙasar ya samu labarin iƙirarin Muluwork kuma ya shirya yi mata gwajin lafiya daga likitoci a Dubai.

A cikin hirar da ta yi da Drew Binsky kwanakin baya, ta yi iƙirarin cewa likitocin ba su samu wani ciwo a jikinta ba, kodayake ba ta ambaci ko sun ba ta lokacin gwaji ba, don ganin ko za ta iya rayuwa da gaske ba tare da abinci da ruwa ba.

“Ba ni da abin da zan ce. Ikon Allah ne kuma na yarda da haka,” in ji Muluwork Ambaw.

Mun ji mutane suna iƙirarrin rayuwa ba tare da abinci mai ƙarfi ba, shekaru da yawa, amma Muluwork Ambaw tana ɗaya daga cikin ’yan ƙalilan da ke iƙirarin cewa ba sa buƙatar abinci ko mai ruwa ne, wanda ke da wuyar gaskatawa.

A cewar Kundin Tarihi na Duniya (Guinness Records), wanda ya fi kowa daɗewa bai ci abinci ko ya sha ruwa ba shi ne mai kwana 18, kuma shi ne mutumin da ’yan sanda suka kama suka manta da shi.

Wannan mata ta yi iƙirarin cewa ta shafe sama da shekara 16 ba tare da cin abinci ko shan ruwa ba.