Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya ce zai kwaso daliban Najeriya da suka makale a kasar Sudan inda yaki ya barke, kyauta zuwa gida.
Rikicin shugabanci ya kazance a Sudan a baya-bayan nan, har ta kai ga rufe sararin samaniyar kasar.
- Halin da daliban Najeriya da suka makale a Sudan suke ci
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Sankarau
Akalla daliban Najeriya 5,000 da ke Sudan sun nuna matukar bukatar a dawo da su gida, inda wasu daga cikinsu ke kokarin tsallaka iyaka zuwa kasar Habasha, mai makwabtaka da Sudan.
Shugaban kamfanin Ake Peace, llen Onyema, ya sanar da cewa idan ’yan Najeriya da ke Sudan za su iya tsallaka iyaka zuwa kasashen makwabtakan Sudan, to kamfaninsa zai kwaso su zuwa gida a kyauta.
Ya ce aikin kwaso su ya wuce a bar wa gwamnati ita kadai, saboda bai kamata a yi asarar dan Najeriya ko daya ba a rikicin na Sudan.
Gwamnatin Tarayya dai ta yi alkawarin ranar Talata za ta fara kwaso ’yan Najeriyan ta kasar Habasha.
Wata sanarwa da Fadar Shugaban Kasa ta fitar ta ce Ma’aikatarta Harkokin Kasashen Waje na aiki da gwamantin kasar Habasha, domin amfani da sararin samaniyarta wajen kwashe ’yan Najeriya da suka makale a Sudan.
A ranar Asabar kungiyar daliban Najeriya da ke Sudan ta bukace su da taru a wasu wurare uku da ayyana domin kwashe su zuwa Habasha.
Tun da farko, wasu daga cikin daliban sun bayyana cewa an fara katse layin sadarwa a Sudan sakamakon rikicin, wanda suka nuna damuwa cewa hakan na iya kawo tasgaro ga yadda za a tuntube su domin kwashe su daga kasar.