Wata mata mai ’ya’ya biyar ta watsa wa ’yar cikinta man fetur sannan ta cinna mata wuta saboda ’yar ta dauki wayar da mahafiyar ta boye a Jihar Ogun.
- An kai shi gidan yari kan satar dunkulen dandanon girki
- An daure mai gadi wata 3 saboda satar naman miya a Abuja
- Mamu ya yi wa matar liman ciki
Makwabcin da suke zaune a gida daya ya shaida wa ’yan sanda cewa matar ta yi wa ’yarta danyen aikin ne saboda wayar dan uwan yarinyar da ta dauko ta ba shi bayan bayan mahaifiyar ta kwace wayar daga hannunsa ta boye.
Ya ce, “Da aka titsiye matar, wadda ta ce sun rabu da mahaifin yaran, ta bayyana wa ’yan sanda cewa ba ta san abin da ya hau kanta ba a lokacin da ta yi wa ’yarta hakan.”
Oyeyemi ya bayyana cewa an garzaya da yarinyar zuwa asibiti mafi kusa inda daga nan aka tura su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Olabisi Onabanjo domin samun kulawar da ta dace.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya sa a tsare matar a Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin gudanar da zuzzurfan bincike.