✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta watsa wa ’yarta fetur ta banka mata wuta

Jami’an tsaron  na Cibil Defence a Jihar Kaduna suna ci gaba da tsare wata mata mai suna Madam Sylbia bisa zargin kona ’yarta mai shekara…

Jami’an tsaron  na Cibil Defence a Jihar Kaduna suna ci gaba da tsare wata mata mai suna Madam Sylbia bisa zargin kona ’yarta mai shekara takwas da man fetur.

Aminiya ta gano cewa gabanin kona ’yar tata sai da ta kulle ta a cikin daki na tsawon kwanaki shida, bayan ta ji mata rauni har sai da makwabta suka kira jami’an tsaro.

Bayanai sun ce mahaifiyar yarinya ta bai wa ’yar tata umarnin kula da daki ne tare da kannenta a lokacin da ita kuma ta tafi kasuwa.

Amma sai yarinyar ta bar dakin ta shiga makwabta kallon talabijin wanda hakan ya sa kannenta suka lalata cikin dakin ita kuma mahaifiyar bayan ta dawo sai ta fusata har ta dauko fetur ta watsa wa yarinyar a jiki ta kunna mata wuta.

Yanzu haka dai ita yarinyar na ci gaba da jinya a wani asibiti da ke Kaduna a karkashin kulawar Ma’aikatar Mata ta Jihar. Kwamishinar Mata da Yara ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce wani ne ya sanar da ma’aikatanta wanda hakan ya sa suka dauki matakin kama matar.

Shi ma Kwamnadan Hukumar Cibil Defence, Modu Bunu ya ce da hukumarsa ta samu wannan labari sai suka aika jami’ainsu domin su taso keyar wadda ake zargin.

A cewarsa, da ake yi wa Misis Sylbia tambayoyi kan dalilan da suka sa ta kona ’yarta sai ta ce wai ’yar ce ba ta jin magana, wanda hakan ya sa take yawan barin dakinsu cikin dauda ta je makwabta wasa, ita kuma abin yana bata mata rai.

Bunu ya ce matar wadda tuni suka shirya  kai ta kotu ta nuna cewa rashin jin yarinyar da kuma yawan fita zuwa wajen kallo ko wasa da kawayenta a makwabta na da alaka da aljanu.