✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta tsattsaga hannun ’yar kishiyarta da reza

Wata mata da ta yi yunƙurin halaka ’yar kishiyarta ’yar kimanin shekara 8, ta shiga komar ’yan sanda. Al’amarin ya faru a Unguwar Onofowokan da…

Wata mata da ta yi yunƙurin halaka ’yar kishiyarta ’yar kimanin shekara 8, ta shiga komar ’yan sanda.

Al’amarin ya faru a Unguwar Onofowokan da ke Ogijo a Jihar Ogun, inda matar mai suna Rose James ta yi wa yarinyar mummunan yanka da reza a sassan hannuwanta biyu.

Mijin matar mai suna Micheal James ne ya ankarar da  ’yan sandan yankin, inda ya shaida masu cewa matar tasa ta kira shi ta wayar salula a lokacin da yake wajen aiki, ta shaida masa cewa ’yarsa Blessing ta doki ƙaramar ’yarta har ta yi mata rauni a ƙafa; don haka za ta ɗauki fansa. Sai ya ce mata ta yi haƙuri har ya dawo amma sai ta ƙi jin maganarsa. Koda ya isa gidan sai ya tarar da cewa ta yi wa yarinyar munanan raunuka a hannayenta da reza, inda nan take kuma ya sanar wa ’yan sanda. 

Ya bayyana cewa DPO na yankin, SP Tijjani Muhammad ne ya jagoranci tawagar ’yan sandan da suka kame wacce ake zargin, inda ta amsa laifinta, cewa aikin Shaiɗan, wanda ya rude ta ga aikata haka.

Tuni dai aka garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Lenard da ke Ogijo, inda likitoci ke kula da lafiyarta, yayin da Kwamishinan ’yan sandan jihar Ogun Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin tasa ƙeyar wacce ake zargin zuwa Sashen yaki da cin zarafin ɗan Adam da cutar da yara domin zurfafa bincike. Ya ce ko kaɗan rundunar ’yan sandan ba za ta saurara wa masu aikata miyagun laifuka a jihar ba.