’Yan sandan jihar Ogun sun kama wata matashiya mai shekara 23 mai suna Mary Olatayo, bisa zarginta da sayar da jaririnta dan mako uku da haihuwa a kan kudi Naira dubu 600.
An kama wacce ake zargin ne biyo bayan korafin da mahaifin jaririn ya shigar a ofishin ’yan sanda na Mowe da ke Karamar Hukumar Obafemi-Owode a jihar.
- Barauniyar jaririyar kwana 3 ta shiga hannu
- An kama daya daga cikin tserarrun fursunonin kurkukun Kuje a Ogun
Kakakin rundunar a jihar, Abimbola Oyeyemi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abeokuta, babban birnin jihar, ranar Alhamis.
Ya ce wanda ya shigar da karar ya shaida wa ’yan sanda cewa, yana da alaka da wacce ake zargin kuma ta samu juna biyu tare da shi.
A cewarsa, ya yi hayar wani gida ne ga wacce ake zargin, inda ta zauna har ta haifi da namiji.
“Shi [mahaifin] ya kara kokawa cewa, ba zato ba tsammani matar ta bace tare da jaririn daga gidan bayan makonni uku da haihuwarsa, sai aka same ta a wani otal inda ta tafi yin hulda da wani mutum.
“Duk kokarin da aka yi na sanin inda jaririn ya kasance bai yi nasara ba,” kamar yadda Oyeyemi ya fada.
Kakakin, ya ce bayan rahoton, Baturen ‘Yan Sanda (DPO) na yankin na Mowe, SP Folake Afeniforo, ya aike da dakarunsa inda lamarin ya faru inda suka cafko wacce ake zargin tare da kai ta ofishin.
Ya kuma ce, “Da aka tsitsiye ta, Mary Olatayo, ta shaida wa ‘yan sanda cewa ta sayar da jaririn ga wani ne a jihar Anambra a kan kudi Naira dubu 600.
“Ta furta cewa, kawarta Chioma Esther Ogbonna ce ta kai ta wurin mai sayen jaririn a Anambra kuma dukkansu sun raba kudin daidai,” in ji shi.
Kakakin ’yan sandan ya ce furucin nata ya taimaka musu suka kai ga kama Chioma, wacce ita ma ta tabbatar da ikirarin na Mary.