Wata mata da ba’a ambaci sunanta ba ta kona `yarta `yar Shekara takwas da fetur a jihar Kaduna.
A yanzu haka matar na tsare a hannun jami’an tsaron sibil defens inda suke ci gaba da bincikenta. Aminiya ta gano cewa matar ta kuma kulle ‘yar tata a cikin daki har tsawon kwanaki shida bayan ta ji mata rauni har sai da makwabta suka kira jami’an tsaron.
Bayanai sun muna cewa Mahaifiya yarinyar ta bai wa diyarta ta umurnin kula da daki ne tare da kannenta a lokacin da ita kuma ta tafi kasuwa domin harkokinta.
Amma sai yarinyar ta bar dakin ta shiga makwabta kallon talabijin wanda hakan yasa kannenta suka lalata cikin dakin, ita kuma mahaifiyar bayan ta dawo sai ta fusata har ta dauko fetur ta watsawa yarinyar a jiki.
Yanzu haka yarinyar na kwance a wani asibiti dake Kaduna inda ake duba lafiyarta.
Kwamishina Mata da kananan yara ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Baba ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce, wani ne ya sanar da ma’aikatanta wanda hakan yasa suka dau matakin kama matar.
Ta kuma nuna alhininta akan wannan halin rashin tausayin da uwar yarinyar ta dauka akan diyar da ta haifa da cikinta.