✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ta kona ’yarta a kan ta cinye abincin kaninta

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta kame wata mata mai suna Misis Madwell kan zargin kona ’yarta mai suna Blessing da dutsen guga mai zafi…

Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta kame wata mata mai suna Misis Madwell kan zargin kona ’yarta mai suna Blessing da dutsen guga mai zafi kan ta cinye abincin kaninta.
 Aminiya ta gano cewa lamarin ya auku ne a cikin barikin kwalejin ’yan sanda da ke unguwar Ikeja a jihar Legas a makon da ya gabata lokacin da Blessing ta dawo daga makaranta tana jin yunwa, sai ta dauki abincin kaninta na goye ta cinye.
Aminiya ta gano cewa da uwar ta lura da laifin da Blessing ta yi sai ta rufe ta da duka ta hada dutsen guga a wutar lantarki ta rika dana mata har sai da ta yi mata raunuka.
Blessing dai tana karatu ne a aji uku na makarantar firamaren gwamnati da ke unguwar Ikeja a jihar Legas kuma mahaifinta sunansa Kofur Madwell da ke aiki a rundunar ’yan sandan jihar Legas.
Asirin Misis Madwell ya tonu ne a lokacin da wani makwabcinsu ya kai kara ma’aikatar mata da rage radadin talauci ta jihar Legas kan halin da Blessing ta shiga sakamakon raunin da mahaifiyarta ta yi mata.
Wani malami a makarantar da Blessing take, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce,  ‘tun ranar Juma’ar da ta gabata muka samu labarin aukuwar lamarin. A lokacin kannen Blessing biyu suna nan sai muka kira su muka tambeye su abin da ya auku, amma sai suka kasa fada mana gaskiya saboda suna tsoron mahaifiyarsu. Daga bisani sun fada mana gaskiyar cewa mahaifiyarsu ce ta kona Blessing da dutsen guga mai zafi. Daga nan sai muka tafi tare da shugaban makarantar inda muka tarar da yarinyar duk jikinta rauni, Da muka tambaye ta sai ta kasa fada mana gaskiyar lamarin, sai muka shiga cikin gidan muka tambayi uwar, sai ta ce mana ruwan zafi ne ya kona ta. Daga bisani da ta ga Blessing za ta tona asirinta sai ta kora ta cikin daki. Daga nan uwar ba ta kara amsa wata tambaya ba’.
Daga nan ne sai ma’aikatar mata da rage radadin talauci ta jihar Legas ta zo da motar daukar marasa lafiya ta dauki Blessing da mahaifiyarta zuwa asibiti.
Daraktan lura da yara na ma’aikatar Misis Fadairo ta ce ba za ta iya cewa komai ba saboda suna asibiti don ceto ran Blessing daga kunar da ta samu.
Duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin mai magana da yawun ’yan sandan jihar Legas ya ci tura, domin wayarta ba ta bugawa.