✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe kanta saboda mahaifinta ya ce ba ’yarsa ba ce

Wata dalibar jami’a da ke karatun digiri na biyu a sashen albarkatun ruwa a Tsangayar Aikin Injiniya ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta…

Wata dalibar jami’a da ke karatun digiri na biyu a sashen albarkatun ruwa a Tsangayar Aikin Injiniya ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta kashe kanta ta hanyar fadawa a kogin Tamburawa da ke Jihar Kano.

Rahotanni sun ce marigayiyar ta kashe kanta ne sakamakon kin amincewa da ita da mahaifinta ya yi a matsayin ’yarsa.

dalibar mai suna Zubaida Nuhu wacce ’yar asalin kabilar Ibira ce bayan kammala karatun digirinta na farko a Jami’ar ABU a shekarar 2014 ta yi aikin hidimar kasa a Hukumar Ruwan sha ta Jihar Kano da ke Tamburawa inda ta kamamla a shekarar 2015.  Daga nan ta sake komawa Jami’ar ABU don zurfafa karatunta inda aka dauke ta a matsayin mataimakiyar malama a sashen.

Binciken Aminiya ya gano cewa an dauki tsawon shekaru ana gudanar da soyayya tsakanin mahifiyar Zubaida da mahaifinta wanda a yanzu haka farfesa ne a wata jami’a da ke kasar nan inda a karshe masoyan suka yi aure. Sai dai auren bai dauki lokaci mai tsawo ba ma’auratan suka rabu inda mahaifiyarta ta tafi da cikinta.

Tun daga lokacin da aka haifi marigayiya Zubaida ne mahaifinta ya ki amincewa ya karbe ta a matsayin ’yarsa, hakan ya sa inji majiyarmu ya sa mahaifiyarta wacce ke zaune a Jihar Kogi ta bayar da rikon marigayiyar ga dan uwanta da ke zaune a Jihar Kano.

Majiyar Aminiya ta ce ko a kwanakin baya sai da marigayiya Zubaida ta kai wa mahaifinta ziyara, a wannan lokacin ma dai bai yarda ya amince ita ’yarsa ba.

Aminiya ta gano cewa bayan Zubaida ta rasu an tsinci wata takarda da ta rubuta inda ta dora alhakin mutuwarta a kan mahaifinta cewa tunda ya ki karbarta a matsayin ’yarsa ba ta ga amfanin ci gaba da rayuwa a hakan ba tare da takamaiman mahaifi ba.

Malam Ibrahim Musa wanda aka fi sani da danliti shi ne shugaban masu aikin yashi a Kogin Tamburawa, kuma yana daya daga cikin wadanda suka tsamo gawar marigayiyar ya shaida wa Aminiya cewa a ranar da lamarin ya faru sun tashi daga aiki sai yara kananan da ke aikin gyaggyara yashin, hakan ya janyo marigayiyar ta samu damar gudanar da aikin da ta kudurta. “Lokacin da ta zo mun bar wurin sai kananan yara ta samu. Don haka yaran sun shaida mana cewa lokacin da ta zo ta tambaye su wurin da ya fi zurfi a kogin su kuma ba su san manufarta ba suka nuna mata. Da suka je wurin sai ta dan zazzagaya sannan ta dawo ta zauna kamar tana hutawa, daga nan su kuma suka yi tafiyarsu. Muna zaton sai wajen yamma lis ko dare kafa ta dauke ne sai ta fada kogin domin a lokacin yaran namu ma sun bar wurin. Mu dai sai da safe aka sanar da mu cewa ga gawar wata mata can a kan ruwa. Da aka duba gefe sai aka ga mayafinta da katinta na ATM. Daga nan muka kira jami’an kwana-kwana da ke Kano suka zo aka tsamo gawarta wacce tuni ta fara lalacewa,” inji shi.

Malam Ibrahim Musa ya kara da cewa “Wurin da marigayiyar ta fada wuri ne mai matukar zurfi, domin ko mu da muke aiki a kogin ba mu zuwa wurin, saboda ko dan uwanka ne ya fada wurin to sai dai ka jira idan gawarsa ta taso sama ka fitar da shi, idan ka ce za ka shiga domin ceto shi, to akwai yiyuwar a yi biyu-babu. Daga nan muka kira

Hukumar Kwana-kwana suka zo aka ciro gawarta, kuma saboda iyayenta sun bayar da cigiyarta a gidan rediyo ya sa aka sanar da su suka zo suk duba suka tabbatar ita ce suka dauki gawarta a kai kai Asibitin Murtala.”

Duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin marikanta da ke Kano abin ya ci tura inda marikinta Alhaji Tajuddeen ya ki cewa uffan a kan lamarin sakamakon daukar mataki da ’yan uwansa suka yi cewa kada kowa ya yi magana da manema labarai.

Shugaban Hukumar Kwana-Kwana ta Jihar Kano, Sagir Madaki ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce “Jami’anmu sun isa Gadar Tamburawa da misalin karfe 10 na safe inda suka fito da gawar marigayiyar mai kimanin shekara 30 daga nan muka dauke ta zuwa Asibitin Murtala inda aka tabbatar da rasuwarta. Daga baya muka damka ta ga iyayenta don yi mata suttura.”