A Lahadin da ta gabata wata mata mai suna Anesthesia Sati, ta haifi ’yan hudu a yankin Karamar Hukumar Shendam da ke Jihar Filato.
Wannan na zuwa ne bayan da Anesthesia ta haifi tagwaye kimanin shekara biyu da suka gabata.
- Tabarbarewar Tsaro: Gombe Ta Kafa Rundunar ‘Operation Hattara’
- Ilimi ya gagari talaka, amma ’yan siyasa na yawo a jiragen alfarma —Gum
Sai dai matar wadda ke da zama a Dulory tare da maigidanta da ya kasance manomi, ta bukaci Gwamnatin Filato da mawadata su tallafa musu domin ba su damar kula da yaran yadda ya kamata.
Shi ma mahaifin yaran, Sati Mairiga, ya roki a taimaka saboda matsalar tsaro ta sa ya baro asalin inda yake da zama a yankin Karamar Hukumar Wase ta jihar wanda hakan ya sa ya rasa komai nasa.
Ya ce, “Dubi irin baiwar da Allah Ya yi mana bayan da muka dawo nan da zama, muna matukar farin ciki. Dan abin da muka mallaka mun baro shi can Wase saboda matsalar tsaro.
“Ina bukatar gwamnati ta taimaka mana, shekara uku ke nan da aurenmu, kuma tsadar rayuwa ta dame mu, muna bukatar taimako domin bai wa kyautar nan da Allah Ya ba mu kulawar da ta dace,” inji shi.