✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Surukin Sarkin Musulmi ya rasu a Landan

Marigayin ya yi gamo da ajalinsa bayan ’yar takaitacciyar jinya a birnin Landan.

Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Sarkin Bichi na Jihar Kano, Alhaji Nasiru Ado Bayero sun yi rashin surukinsu, Abubakar Imam Galadanchi.

Abubakar Imam Galadanchi ya rasu ne bayan ’yar takaitacciyar jinya a birnin Landan da ke Birtaniya.

Jami’in hulda da jama’a na Fadar Sarkin Musulmi, Aminu Halliru ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da wakilinmu.

A cewarsa, Sarkin Musulmi da kuma Sarkin Bichi na auren ’ya’yan marigayin wanda mai yankan kauna ta debewa tsammani.