Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta kasa (NFF) ta kusa kammala shirye-shirye wajen shirya wa kungiyar kwallon kata ta kasa Super Eagles wasannin sada zumunta biyu da kasashe biyu a watan gobe watau na Maris, 2015.
Sai dai kawo yanzu Hukumar ba ta ambaci kasashen biyu da kungiyar za ta fafata da su a wasannin ba amma ana sa ran za ta bayyanasu kafin karshen wannan wata da muke ciki na Fabrairu.
Sakatare Janar na hukumar NFF Musa Amadu ne ya tabbatar wa manema labarai haka a ranar Litinin da ta wuce a Abuja a lokacin da yake yi musu bayani.
“Ina tabbatar muku da cewa Hukumar NFF ta kuduri aniyar shirya wasannin sada zumunta biyu da kasashe daban-daban ga kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles a watan gobe”.
“Idan komai ya kammala za mu sanar da ku kasashen da kuma wurin da wasannin za su gudana za a yi su walau a cikin gida ko kuma a wajen kasa”.
“Mun fara yin gyara a kungiyar ta Super Eagles ne da wasannin sada zumunta biyu da muka yi a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) inda muka buga da kasashen Kwaddebuwa da kuma Yemen don haka ne muke kokarin shirya wadansu wasannin sada zumunta biyu a watan gobe”, inji shi.
kasar Brazil dai ta janye daga yunkurin da Super Eagles ta yi ne na yin wasan sada zumunta da ita a watan gobe na Maris, inda Brazil din ta maye gurbin Najeriya da kasar Chile. Hakan ta sa Najeriya take kokarin samun wadansu kasashe biyu don yin wasannin sada zumuntar.
Super Eagles za ta yi wasannin sada zumunta biyu a watan gobe
Hukumar shirya wasan kwallon kafa ta kasa (NFF) ta kusa kammala shirye-shirye wajen shirya wa kungiyar kwallon kata ta kasa Super Eagles wasannin sada zumunta…