A ranar Juma’ar da ta wuce ne tsofaffin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta lallasa ta masu wasan kwaiwayo da waka da ci 4-0 a wasan sada zumuntar da Hukumar kula da kare hakkin dan Adam ta shirya a Abuja.
Wasan ya kayatar bayan da ’yan kallo suka cika filin wasa da ke Abuja don kashe kwarkwatar idanu.
An shirya wasan ne don fadakar da al’umma muhimmancin kula da kare hakkin dam Adam.
Daga cikin tsofaffin ’yan kwallon Super Eagles da suka buga wasan akwai Taribo West da Austin Okocha da Mutiu Adepoju da Stephen Keshi da Daniel Amokachi da Alloy Agu da Peter Rufa’i da Eammnuel Amunike da kuma Austin Eguaboen.
A bangaren masu wasan kwaikwayo da waka wadanda suka buga wasan sun hada da shahararren ‘yan wasan barkwanci AY & Okey Bakassi, da Emeka Enyoocha da Fred Amata da Moses Inwang da MI Abaga da sauransu.
Super Eagles ta lallasa kungiyar wasan kwaikwayo da ci 4-0
A ranar Juma’ar da ta wuce ne tsofaffin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta lallasa ta masu wasan kwaiwayo da waka da ci 4-0…
