Kulob din Sunshine Stars na Akure ya fara yunkurin dauko sabon koci daga waje wanda zai maye gurbin tsohon koci Kennedy Boboye da ya ajiye aiki.
Shi tsohon kocin ya ajiye aikinsa ne jim kadan bayan an kammala kakar wasa ta bana.
Jaridar da ke buga labarin wasanni Completesportsnigeria ta kalato cewa wani jigo a kulob din ne ya kyankasa mata wannan labari cewa kulob din ya fara tunanin dauko sabon koci daga waje ne kafin a fara kakar wasa mai zuwa.
“Ba mu ji dadin yadda muka gama kakar wasan da ta wuce ba duk da kwazon da muka nuna a farkon gasar, amma daga baya sai al’amurra suka rincabe mana. A kokarin da muke yi na ganin mun bunkasa harkar kwallo a kulob din ce ta sa muka yanke shawarar dauko sabon koci daga waje”, inji shi.
Kulob din Sunshine Stars dai yana fafatawa ne a gasar rukuni-rukuni ta kasa.
Sunshine Stars za ta dauko koci daga waje
Kulob din Sunshine Stars na Akure ya fara yunkurin dauko sabon koci daga waje wanda zai maye gurbin tsohon koci Kennedy Boboye da ya ajiye…