✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sunayen Sarakunan Katsina

A wannan mako mun muku jerin sunayen sarakunan da suka mulki masarautar Katsina tun daga kan Habe zuwa Sarakunan Fulani. Sannan muka tsakoro muku kadan…

A wannan mako mun muku jerin sunayen sarakunan da suka mulki masarautar Katsina tun daga kan Habe zuwa Sarakunan Fulani. Sannan muka tsakoro muku kadan daga cikin tarihin Sarki Muhammadu Korau Sarkin Katsina na bakwai daga cikin Sarakunan Habe.

Sarkunan Haɓe

Gidan Durɓawa

  • Sarkin Katsina Kumayau
  • Sakin Katsina Rumba Rumba
  • Sarkin Katsina Bataretare
  • Sarkin Katsina Jin Marata
  • Sarkin Katsina Yankatsari
  • Sarkin Katsina Jibda Yaƙi (Sanau)

Gidan Korau

  • Muhammadu Korau 1348 – 1398
  • Usman Maje 1398 – 1405
  • Ibrahim Soro 1405 – 1408
  • Marubuci 1408 – 1426
  • Muhammadu Turare 1426 – 1436
  • Ali Murabus 1436 – 1462
  • Ali Karya 1462 – 1475
  • Usman Tsaga Rana 1475 – 1525
  • Usman Damisa Gudu 1525 – 1531
  • Ibrahim Maje 1531 – 1599
  • Malam Yusufu 1599 – 1613
  • Abdulƙadir 1613 – 1615
  • Ashafa 1615 – 1615
  • Gabdo 1615 – 1625
  • Muhammadu Wari 1625 – 1637.
  • Muhammadu Tsaga Rana 1637 – 1649
  • Mai Daraye 1649 – 1660
  • Sulaiman 1660 – 1673
  • Usman Tsaga Rana 1673 – 1692
  • Toyariru 1692 – 1705
  • Yanka Tsari (Uban Yara I) 1705 – 1708
  • Uban Yara II 1708 – 1740
  • Jan Hazo (Dan Uban Yara) 1740 – 1751
  • Tsaga Rana 1751 – 1764
  • Muhammadu Kayiba 1764 – 1771
  • Karya Giwa 1771 – 1788
  • Giwa Agwaragi 1788 – 1802
  • Gozo 1802 – 1804
  • Bawa ɗan Giwa 1804 – 1805
  • Muhammadu Maremawa 1805 – 1806
  • Magajin Haladu 1806 – 1807

Sarakunan Fulani

Dallazawa:

  • Umarun Dallaje 1807 – 1835
  • Muhammadu Bello 1835 – 1844
  • Saddiƙu 1344 – 1869
  • Ahmadu Rufa’i 1869 – 1869
  • Ibrahim 1869 – 1882
  • Musa 1882 – 1887
  • Abubakar 1887 – 1905
  • Yero 1905 – 1906

Sulluɓawa

  • Muhammadu Dikko 1906 – 1944
  • Usman Nagogo 1944 – 1981
  • Muhammad Kabir Usman 1981-2008
  • Abdulmumini Kabir Usman 2008 zuwa yanzu

Wane ne Muhammadu Korau?

Sarkin Katsina Muhammadu Korau, shi ne Sarki na bakwai a jerin sarakunan Katsina. Sarki Muhammadu Korau Haɓe ne kuma Musulmi. Ya zo a ruwayar Ingawa (2006), cewa shi Sarki Muhammadu Korau ɗan asalin garin Tsafe ne da ke Jihar Zamfara ta yau. Sarki Muhammadu Korau ya hau gadon sarautar Katsina bayan da ya kayar da Sarki Sanau a kokawar da suka buga.

A zamanin Sarki Korau ne aka gina Masallacin Juma’a na farko a garin Katsina, wanda wannan masallaci daga baya ya bunƙasa ya koma wata babbar jami’ar karantar da addinin Musulunci. A cikin wannan masallaci akwai wata hasumiya mai tsawo wacce ake kira da Hasumiyar Gobarau.

Mun ciro wannan rubutu ne daga: Ingawa T.L. (2006). Katsina a History of an Ancient City. Hamdala Prinitng and Publishing da kuma shafin Intanet.