✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sun yi wata 8 suna gudanar da ofishin ’yan sanda na bogi a otel din Indiya

Wannan ne karo na farko da aka bude ofishin 'yan sanda na jabu a kasar

‘Yan sandan kasar Indiya sun kama wasu mutum shida da suka shafe wata takwas suna sojan gona a matsayin ‘yan sanda, har suka bude ofishin jabu a wani Otel, suna karbar kudi a hannun mutane.

Tuni sojojin gonar da suka hada da mata biyu da maza hudu, suka shiga hannu, kodayake shugabansu ya cika wandonsa da iska.

Sojan gona a aikin dan sanda ba sabon abu ba ne a Indiya, sai dai wannan ne karo na farko da aka samu wanda ya bude ofishin ‘yan sanda na jabu.

Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Kasar, Srivastava ya shaida wa manema labarai cewa mutanen dai sun bude ofishin ne a jihar Bihar, wanda bai nisan mita 500 daga gidan Shugaban Rundunar ba.

Rahotanni dai na nuna suna daukar bindigun gargajiya da lambobin girmamawa na kayan ‘yan sandan gaske.

Kazalika, suna karbar kudade a hannun mutane da sunan kwato musu hakkinsu, ko kuma inshorar gidaje ko samar musu aikin dan sanda.

Baya ga haka, suna biyan mutanen unguwar Rufi 500 domin sojan gona a matsayin ‘yan Sanda.

Dubun mutanen dai ta cika ne bayan ‘yan sandan kasar sun hange su da bindigun gida a madadin na gaske da aka san ‘yan sanda na asali na amfani da su.