An bayar da belin wani Ba’indiye da ake zargi da yunkurin yin fyade bisa sharadin ya wanke tufafin matan da ke kauyensu na tsawon wata shida.
Wanda aka yanke wa hukuncin mai suna Lalan Kumar, mai shekara 20 zai sayi omo da sauran kayayyakin da ake bujata domin wankin tufafin mata 2000 a kauyen Majhor na Jihar Bihar.
- Subodh Singh: Likitan da ya yi wa yara 37,000 tiyata kyauta a Indiya
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram sama da 40 a Borno
Kumar, wanda yake sana’ar wanki da guga, an kama shi ne a watan Afrilun bara bisa zarginsa da yunkurin fyake, kamar yadda jami’in dan sanda Santosh Kumar Singh a Gundumar Madhubani a Bihar ya sanar.
Shugabar Karamar Hukumar yankin da lamarin ya faru mai suna Nasima Khatoon ta ce, “Dukkan matan kauyen sun yi farin ciki da hukuncin da kotu ta yanke. Hakan zai kara mutunta mata da kuma taimakawa wajen kare mutuncinsu,” inji Khatoon, daya daga cikin jiga-jigan jauyen da za su sanya ido kan Kumar.
Anjum Perween ya ce, “Matan kauyen sun ce, wannan umarni ya yi tasiri sosai ta hanyar sa aikata laifuffukan da suka shafi mata su zama ababen tattaunawa a cikin al’ummarsu. Wannan mataki ne na ban-mamaki kuma wani nau’in hukunci na daban da ke aika sako ga al’umma.”
An yi wa dokar fyade ta kasar Indiya garambawul bayan wani fyade da aka yi wa wadansu rukunin mata a birnin New Delhi a shekarar 2012, amma har yanzu yawan aikata laifuffukan yana karuwa, inda aka samu rahotannin fyade sama da dubu 28 a shekarar 2020.
An dade ana zargin ’yan sanda da rashin yin abin da ya dace don hana miyagun laifuffuka faruwa da kuma kasa gabatar da kararrakin cin zarafin mata a kotu.
Daga guardian.ng