’Yan sandan sun gurfanar da wasu mutum uku bisa zargin tono gawarwaki 10 a makabarta suka kuma datse musu kawuna domin yin tsafi.
’Yar sanda mai gabatar da kara, Sufeto Monica Ikebuilo, ta ce mutanen sun yi tsafi ne da sassan jikin gawarwakin da suka tono a makabartar Cocin St Paul Anglican Church da ke Orun-Ekiti.
- Suna neman hana a hukunta wanda ya yi wa ’yarsa fyade
- Bidiyon fyade: An tsare dan hadimin Tambuwal a kurkuku
Ta bayyana wa Kotun Majistare da ke zama a Ado-Ekiti cewa an aikata laifin ne tsakanin watan Maris da Satumba 2020.
Jami’ar ta ce, laifin ya saba wa Sashe na 242(1) b, 210(e) da 213(b) na Dokar Manyan Laifukan Jihar Ekiti na 2012.
Mai gabatar da karar ta bukaci kotun da ta tsare wadanda ake zargin mutanen a kurkuku har sai an samu shawarar Ofishin Hukumar Shigar da Kara ta jihar (DPP).
Mai Sharia Adefumike Anoma, ta umarci a tsare wadanda ake zargin a gidan yari zuwa lokacin da aka samu shawara daga ofishin.
Alkalin ta kuma ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Nuwamba, 2020.