Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta yi bajekolin wasu mutum uku da ta ce an kama su ne da zargin karkatar da akalar wata tirela da ke makare da bandir-bandir na shimfidun kafet a Jihar.
A cewar rundunar, darajar kayan ta kai kimanin Naira miliyan 550.
Kakakin Rundunar, Mista Olawale Osifeso, ya ce wadanda ake zargin, masu suna Moses Olatunji da Lawal Adesina da Teslim Olapade, an kama su ne a maboyarsu da ke kan titin Ring Road a Ibadan, babban birnin Jihar.
Ya ce a lokacin da aka kama su, an yi nasarar gano wannan kaya da kuma motar tirelar da suka yi amfani da bindiga wajen tilasta wa direbanta karkatar da akalarta zuwa maboyar tasu.
Jagoran wadannan barayi, Moses Olatunji, bai musanta laifin da ake zargin su da aikatawa ba.
Ya shaida wa ’yan jarida cewa wannan ba shi ne kame na farko da aka yi masa ba.
Moses ya ce an sha kama shi a kan irin wannan laifi da yake yi a kan babbar hanyar Ibadan zuwa Legas.
Su ma Lawal Adesina da Teslim Olapade ba su bata lokaci ba wajen fadin irin rawar da suka taka a aika-aikar.
Mutum ukun dai na cikin guda 31 da rundunar ta yi bajekolin nasu. Sauran wadanda ake tuhumar kuma an same su da kayayyakin da suka hada motoci da babura da makamai, kuma ana zarginsu da aikata fashi da makami da garkuwa da mutane a sassa daban-daban na Jihar ta Oyo.