Wasu matasa su biyu masu shekaru 20 da 24 sun sace wani yaro ɗan shekara 12 a garin Dankama na Ƙaramar Hukumar Kaita ta Jihar Katsina a ranar 11 ga wannan wata da misalin ƙarfe 8 na dare.
Matasan sun yi karo da yaron mai suna Salihu ne a hanyarsa ta zuwa wani shagon magani inda ba tare da ɓata lokaci ba suka yi awon gaba da shi.
Daga bisani suka kira mahaifinsa suna neman Naira miliyan 25 kafin su sako shi, kamar yadda ɗaya daga cikinsu ya shaida wa manema labarai a hedikwatar ’yan sandan Jihar Katsina.
Ɗaya daga cikinsu mai lakanin Auta ya ce, bayan da mahaifin yaron ya nuna cewar ba shi da kudi ya shaida wa abokinsa Ƙwalwa, halin da ake ciki domin shi ne wanda ya yi kiran wayar.
“Daga nan sai dai na ji yaron ya mutu wanda nike zaton ko shi Salihu ya gane Auta shi ya sa ya kashe shi.”
Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce bayan samun labarin ɓacewar yaron tare da tsintar gawarsa suka baza komarsu domin kamo waɗanda suka yi wannan ta’asa har suka kamo waxannan matasa da ake zargi.
“Muna cikin bincike wanda da zarar mun kammala, za mu miƙa su kotu domin ɗaukar mataki na gaba,” in ji shi.