✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sultan ya roki limaman Juma’a su yi hudubar zaman lafiya

Sarkin Musulmi ya ce yin zanga-zanga bai dace da koyarwar addinin Musulunci ba

Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci a Najeriya, ta bukaci limaman Juma’a a fadin Najeriya da su shirya hudubarsu ta Juma’a mai zuwa 23 a kan muhimmancin zaman lafiya da yi wa kasa addu’a.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III ya aike da sakon ta bakin Shugaban Kwamatin Watsa Labarai na Majalisar, Alhaji Femi Abbas.

Sarki Musulmi ya kirayi al’ummar Musulmi da su rungumi zaman lafiya, su kaurace wa tayar da fitintinu ba gaira ba dalili.

Ya ci gaba da cewa ba yadda al’uma za ta samu ci gaba muddin ba ta cikin zaman lafiya, don haka ya bukaci jama’a da su dukufa wurin yi wa kasa addu’ar samun hadin kai da mutunta juna.

Da yake magana a kan zanga-zangar #EndSARS, Sarkin Musulmin ya ce zanga-zanga ba ta daga cikin koyarwar Musulunci.

Saboda haka ya bukaci limamai da daidaikun mutane da su dukufa wurin yin addu’o’in zaman lafiya da kauce wa shiga hakkin wasu ko taba dukiyar wani babu gaira babu dalili da sunan zanga-zanga.