✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sulhu da ’yan bindiga: Dalilin da Gumi da El-Rufa’i suka yi hannun riga

Gwamnan yana mayar da martani ne kan bukatar Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ta a yi wa ’yan bindigar afuwa.

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa ba za ta yi sulhu da ’yan ta’adda da ke kashe mutane ba, inda ya ce duk wani dan ta’adda da aka kama kashe za a yi.

Gwamnan ya bayyana haka ne a zantawarsa da Sashin Hausa na Gidan rediyon BBC, inda ya ce ba zai ba da diyya ko yafiya ga masu kashe mutane ba domin babu wanda ya yi musu laifi.

Gwamnan yana mayar da martani ne kan bukatar fitaccen malamin nan na Kaduna Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ta a yi wa ’yan bindigar afuwa don kawo karshen kashe-kashen da suke yi a yankin.

Babu hadin kai tsakanin gwamnonin Arewa maso Yamma

Game da yadda za a yaki ’yan ta’addan, Gwamna El-Rufa’i ya ce har yanzu babu hadin kai a tsakanin gwamnanonin Arewa maso Yamma domin wadansunsu na ganin tattaunawar sulhu da ’yan ta’addan ne mafita, yayin da wadansu ke ganin hakan ba zai taimaka ba.

Sai ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta taimaka da sojoji da sauran jami’an tsaro su shiga dajin a kashe ’yan ta’addan.

Ya ce Jihar Kaduna na tattaunawa da Jihar Neja domin kusan kullum suna ganawa da Gwamnan Jihar a kan yadda za a samu mafita.

“Wadansu gwamnoni suna so a yi sulhu da yafiya sannan a ba da diyya, wadansu ba sa so. Mu a Jihar Kaduna idan ka sace mutum ka yi nasara to, idan muka kama ka kashe ka za mu yi domin muna cikin yaki ne da ’yan ta’adda. Jihar.

Zamfara kuwa su sun yarda da sulhu hakan ya sa akwai bambanci a tsakanin mu gwamnoni,” inji shi.

Gwamnan ya ce duk wanda yake ganin mai garkuwa da mutane zai koma rayuwarsa ta da wadda sai ya sayar da sa a shekara zai samu Naira dubu 100 yana yaudarar kansa ne.

Ya ce game da batun biyan diyyar, “diyyar me? Laifin me aka yi musu. Su da suke kashe mutane suke kone gidajensu kuma suke neman diyya. Sheikh Ahmad Gumi abokina ne, kuma mun yi magana da shi na fada masa cewa yawancin Fulanin nan ba su da addini, mun kama da yawa daga cikinsu da ko Fatiha ba su iya ba.

“Maganar da muka yi da shi Malam ke nan amma abin da ya je yana yi cewa a yafe musu ba mu yarda da wannan ba,” inji shi.

Ba dukkansu ba ne ’yan ta’adda – Dokta Gumi

Sai dai a martanin Sheikh Ahmad Gumi kan matsayar ta Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa rashin fahimtar addini da ’yan ta’addan ke fama da shi ba hujja ba ce da za a rika amfani da ita ana kashe su.

Dokta Gumi ya ce ’yan ta’addan sun kasu kashi uku ne; akwai kananan barayi da ’yan fashi da makami sai kuma ’yan ta’adda.

Ya ce kashi 90 sun fi yawa a ta’adanci saboda an yi musu rashin adalci an zalunce su an kuma kashe na kashewa.

Sannan idan suka fita kiwo suna samun matsala da manoma. Hakan ya sa suka dauki makamai domin kare kansu. A cewar malamin, sun ga abin da ake yi wa Fulani a Jihar Oyo inda aka kona musu rugarsu a yayin da wadanda suke lalata musu rugagen suke zaune a manyan gidaje a cikin gari.

“Saboda haka, rashin ba su damar jin dadin arzikin kasa na daya daga cikin abin da ya jefa su cikin sata da garkuwa da mutane tare da ta’adanci. Don haka kuskure ne a ce dukkansu ’yan ta’adda ne saboda haka akwai bukatar gwamnati ta ba su kula ta musamman da kuma yafiya.

“Ba maganar masu laifin nake yi ba”

“Ni ba da yawun masu aikata laifuffuka a cikinsu nake magana ba saboda akwai barayi da ’yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane a cikin kowace kabila. Akwai a Yarbawa da Ibo, saboda haka ba za mu boye duk wani mai aikata laifi ba a cikin Fulani, amma kuma ba za a zargi dukkansu ba. Abin da muke cewa ke nan,” inji shi.

Kan cewa Gwamnan Kaduna na ganin ba a yi wa Fulanin laifi ba, don haka babu zancen yafiya ko biyan diyya sai Sheikh Gumi ya ce, “Babu wanda ya ce a biya ’yan ta’addan cikinsu diyya. Kashi 90 na Fulani an aikata musu laifi. Sun rasa iyayensu da dabbobinsu da gidajensu, don haka akwai bukatar a biya irin su diyya.”

Game da cewa ba su da ilimin addinin Musulunci. Sheikh Gumi ya ce hakan ba yana nuna cewa idan mutum ba ya da ilimin addini shi ke nan sai ka kashe shi.

Malamin ya ce akwai nasarar a hanyar da suke bi na kawo karshen matsalar.

“Ban dade da fitowa daga cikin daji ba a Jihar Zamfara kuma duk mun gana da su. Kuma sun ce a shirye suke su ajiye makamansu muddin suka samu tabbacin kariya daga gwamnati domin su ci gaba da zaman lafiya da Hausawa,” inji shi.

Game da batun ci gaba da karantar da Fulanin kawai a Kaduna, maimakon zagaye jihohin da yake yi, sai ya ce, a Jihar Kaduna ba su samu taimakon gwamnati ba. Ita kuma Jihar Zamfara ta gayyace shi ne domin su je su taimaka mata.

“A Jihar Kaduna mun yi kokarin amfani da kudin aljihunmu ne domin gina musu makarantu, gwamnatin ba ta taimaka ba. Amma su nan su ne suka nemi a je a taimaka musu.

“Da aljihunmu muke kokarin samar musu da rijiyoyin burtsatse da gina musu makarantu. Muna nan a kan bakarmu ta ilimantar da su ba mu kauce manufa ba. Shi ya sa duk inda muka je muke raba musu littattafai kuma suna karba domin suna son koyo,” inji shi.

“Ba za mu juya musu baya ba ina da hotunan wata ’yar yarinyar da ke shan ruwa a cikin kududdufin da dabbobi ke sha. Makaranta da dakin haihuwa da aka gina musu shekaru masu yawa duk sun lalace. Ba su da komai na jin dadin rayuwa. Ka samar musu da abubuwan rayuwa kafin ka fara maganar kashe mutane,” inji shi.

Game da ko akwai siyasa cikin tafiyarsa ganin akwai ’yan siyasa a ayarinsa, Dokta Gumi ya ce “Ko kadan babu siyasa domin akwai kusan kowa cikin tafiyar. Babu abin da ya hada tafiyar da siyasa.

“Akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta kashe kudi wajen samar musu da abubuwan more rayuwa domin a halin da ake ciki ba su da komai a daji. Ku ba su kasonsu daga arzikin kasa kafin ku nemi biyayyarsu a gwamnatance. Kuna zaune cikin manyan gidaje a birane amma kuna son su bi ku.

“Suna cikin mummunan talauci, an wulaqanta su, an yi watsi da su. A maimakon sayen jiragen yaki, me zai hana a yi amfani da kudaden wajen gina musu makarantu da asibitoci da hanyoyi. Ba mu goyon bayan masu aikata laifi,” inji shi