Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce rashin rashin shugabanci mai adalci a Najeriya ne ya haifar da yunkurin ballewa da kuma surutai kan mulkin karba-karba tsakanin shiyyyoyin Najeriya.
Sule Lamido, a yayin wata hita ta musamman da Aminiya ta yi da shi ya ce lokacin mulkin karba-karba a Najeriya ya wuce, yanzu lokaci ne na a bayar da mulki ga wanda zai iya samar da jagoranci nagari ba maganar yankinsa ko addininsa ko kabilar da ya fito ba.
- ‘Akwai yuwuwar kudin kiran waya da na data ya karu a Najeriya’
- Marasa gaskiya ke komawa APC — Sule Lamido
“In kana maganar aikin kasa, cigaban kasa, gina kasa, inganta rayuwar mutane, zaman lafiya mu yi suna a ko’ina a duniya, kamata ya yi a ce a koma bangaren wa zai iya? wa ya dace ya yi?
“Ko Inyamuri ne ko Bahaushe ko Angas ko dan Fulani ko Kirista, shi ne a kalli wanda zai iya din.”
Tsohon ministan wanda kuma uba ne a jam’iyyar PDP ya ce ko a shekarar 1999 da jam’iyyar ta bullo da batun karba-karba, an yi ne domin ana da shugabanni masu hangen nesa da suga akwai bukatar yin hakan a wancan lokacin.
“Maganar mulkin shiyya-shiyya da ake yi yana da tarihi fa, akwai hujjar da ta sa aka yi shi da:
“Tun da lokacin da aka yi da din shi ne an yi zabe na ‘June 12’ Abiola ya ci zabe an soke, shi ake ganin kamar mu ’yan Arewa muka hana shi.
“Saboda haka da za a sake komawa mulkin farar hula muka ce shin ya za a yi muga wannan kurjin ko wannan ciwo na ‘June 12’ an yi magain sa? Shi ne aka ce a kai mulkin nan kasar Yarabawa, A PDP ke nan. Wannan shi ne hikima.
“A wannan lokaci duk jam’iyyun guda uku — AD da PDP da APP — suna da shugabanni masu hikima, masu basira, masu hangen nesa; Abun da muka yi a PDP ya sa mutanen AD da APP suka ce tunda abokanmu sun yi wannan abu don zaman lafiya mu ma ya kamata mu yi.
“Wannan ya sa a wancan lokacin duk ’yan takarar suka fito daga kasar Yarabawa.
“Wannan an yi ne saboda a hikimar wancan lokacin da wasu shugabanni masu adalci, masu hangin cewa, masu cewa a yi maganin abin da ciwon da ke damun Najeriya na soyayya da zumunci da yarda,” kamar yadda ya bayyana.
Lokacin mulkin karba-karba ya wuce
Sule Lamido ya ce a yanzu bayan shekara 23 bai ma kamata a dawo da maganar mulkin karba-karba ba sai dai idan ana nufin fahimtar junar da aka yi a baya lokacin zaben 1999 bai wadatar ba.
“Maganar ita ce dayan biyu; ko dai har yanzu akwai wancan ciwon bai warke ba, to sai a yi shi — kama-kama — cewa har yanzu ana bukatar sulhu, wanda ke nufin ba a maganar aikin kasa ke nan sai dai maganar sulhu.
“Maganar aikin kasa, cigaban kasa, gina kasa, inganta rayuwar mutane, zaman lafiya mu yi suna a ko’ina a duniya, kamata ya yi a ce a koma bangaren wa zai iya? Wa ya dace ya yi?
“Amma in ana ganin cewa har yanzu ba mu kai matsayin da za a yi maganar iyawa ba, sai maganar maganin fushi, maganin cewa sai nawa ne, ko kaza-kaza, to a je a yi ta yi!
“Amma maganar ita ce har yaushe za a ce a’a ni nawa zan yi? Ina maganar kasar kuma?”
Yadda Najeriya ta shiga tsaka mai wuya
Da ya juya kan batun masu neman ballewa domin kafa kasashen Biyafra da kuma Jamhuriyar Oduduwa, da kuma matsalar tsaro a Najeriya, Sule Lamido ya ce duk abu daya ne ya haifar da su.
“Ko’ina a Nejeriya akwai wadannan masifun, saboda haka maganar ita ce me ya kawo su? Shugabanci mara adalci.
“Idan akwai shugabancin da yake ya san abin da ya san hakkin mutane da ba su hakkinsu, wallahi wadannan abubuwa ba za a yi su ba,” inji shi.