Sufeto Janar na rundunar ’yan sandan Najeriya ya bayar da ummarnin a yi wa rundunar tsaro ta musamman da ke yaki da fashi da makami garambawul sakamakon koken da jama’a suka rika yi na yadda jami’an rundunar ke gudanar da ayyukansu.
Mai Magana da Yawun Rundunar, Jimoh Moshood shi ne ya bayyana haka a sanarwar da ya raba wa manema labarai a Abuja.