Wani rahoton Kafar Labarai ta BBC ya ce kasar Sudan ta kwashe wasu jiragen yakinta daga wani muhimmin sansanin sojojin sama na kasarta domin bai wa jiragen yaki na kasar Rasha damar kafa nasu sansanin.
Rahoton ya ambato wata jaridar Intanet mai suna Al-Rakoba mai alaka da jam’iyyun siyasa masu adawa da gwamnatin mulkin soja ta kasar Sudan tana cewa Rasha za ta jibge jiragen yakin ne da jiragen da ke jigilar kayan yaki a sansanin a karkashin wani shiri na kai samame a wani wurin da ba a fayyace ba.
Jaridar ta Al-Rakoba ta kuma ce wani babban hafsan sojin Sudan ya shaida mata cewa an kwashe jiragen yakin na Sudan ne daga sansanin Wadi Seidna da ke Arewa da Omdurman zuwa wasu filayen jiragen sama da suke wajen Khartoum.
Hafsan ya kuma ce Rasha za ta ajiye sansani daya ko biyu na sojojin samanta a sansanin na Wadi Seidna.
Mataimakin Shugaban Sudan Mohamed Hamdan Dagalo wanda ake yi wa lakabi da Himidti ya ziyarci Rasha a cikin ’yan kwanankin da suka gabata inda ya tattauna da jami’an Rashar kan batutuwan inganta tsaro.