✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Suarez ya koma Celta Bigo

Dan kwallon tsakiya a kulob din FC Barcelona na Sifen, Denis Suarez ya canja sheka zuwa kulob din Celta Bigo da ke Sifen. Kamar yadda…

Dan kwallon tsakiya a kulob din FC Barcelona na Sifen, Denis Suarez ya canja sheka zuwa kulob din Celta Bigo da ke Sifen.

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, dan kwallon ya koma Celta Bigo ne a kan Yuro miliyan 13 (kimanin Naira biliyan 52 da miliyan 91) sannan akwai yiwuwar a kara masa Yuro miliyan 3 (kimanin Naira biliyan 12 da miliyan 21) idan ya yi kokari.

Kungiyoyin biyu sun tabbatar da kulla yarjejeniyar sayar da dan kwallon a tsakaninsu a ranar Litinin da ta wuce.