Shahararren dan kwallon FC Barcelona da ya canza sheka daga kulob din Liberpool a karshen kakar wasan da ta gabata ya fara shirin yin wasansa na farko a kulob din a ranar 25 ga wannan wata watau a ranar da za a gwabza a tsakanin kulob din da na Real Madrid a gasar rukunin La-Liga da ake wa lakabi da El-Classico.
Shi dai Suarez dan asalin Uruguay, an yanke masa hukuncin dakatar da shi daga yin wasanni har na tsawon wata hudu ne bayan an same shi da laifin cizon dan kwallon Italiya Giorgio Chiellini a gasar cin kofin duniya da ya gudana a Brazil. Daga baya ne aka kyale shi ya rika yin atisaye da kuma buga wasannin sada zumunta bayan ya daukaka kara a kotun sauraren kararrakin wasanni ta duniya (Court of Arbitration for Sport).
A ranar Litinin da ta gabata ne ya zura kwallaye biyu daga cikin ukun da kasarsa Uruguay ta zura a ragar Oman a wasan sada zumunta bayan an tashi 3-0.
Shi ma daya daga cikin ’yan kwallon FC Barcelona Andre Iniesta ya bayyana Suarez a matsayin dan kwallon da zai taimaki kulob din Barcelona wajen samun nasarar lashe kofuna a kakar wasa ta bana.