✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Su wa suka cancanci mu zaba a 2023?

Masu iya magana suka ce, kowa ya yi da kyau, zai ga da kyau.

Malam Ahmed Mahmud wanda aka fi sani da Sa’adu Zungur, a cikin wakarsa ta ‘Arewa Jumhuriyya ko Mulukiya’ yana cewa: “Mu dai hakkinmu gaya muku, Ko ku karba ko ku yi dariya.

“Dariyarku ta zam kuka gaba, Da ladamar mai kin gaskiya.”

Don haka za mu sauke wannan hakkin, idan Allah Ya sa al’umma sun fadaka sun zabi wadanda suka cancanta, rayuwarsu da ta ’ya’yansu ta inganta.

Idan kuma suka yi dariya suka biye wa son zuciyarsu suka sayar da ’yancinsu ta hanyar karbar ’yan dubban da ba za su wadace su a tsawon shekara hudu ko idan aka kai su a asibiti ba, dariyarsu ta zame musu kuka da nadama a tsawon wadannan shekaru da za a kwashe ana mulkar su.

Don haka, idan kunne ya ji, jiki ya tsira.

To, a yanzu haka an buga kugen siyasa, masu neman kuri’unku za su fara bazama neman goyon bayanku da kuma kuri’unku.

A sama muna da wasu ’yan takara da za su kara a kan neman kujerar shugabancin kasa.

Manyan kuma sanannu daga cikinsu, su ne, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso na Jam’iyyar NNPP da Asiwaju Bola Tinubu na Jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.

Akwai kuma Peter Obi na Jam’iyyar LP da kuma Hamza Al-Mustapha na Jam’iyyar AA; sai kuma sauran ’yan takara da ba a san su sosai ba a kasar.

Sannan a kowace jiha akwai ’yan takara biyu ko fiye da haka wadanda suke neman kujerar gwamna.

Don haka, idan muka tashi zabe, ba za mu kalli wani dan siyasa ba a karan kansa, ba kuma za mu zabi wadanda muke so ba. Za mu zabi wadanda suka cancanta ne ko da kuwa ba ma kaunarsu.

Za mu zabi wadanda Najeriya ce a gabansu ba wata kabila ba. Wadanda Najeriya ce a gabansu ba wani addini ba. Wadanda Najeriya ce a gabansu ba wani sashe na mutane ba.

Yana daga abin da ya dinga mayar da mu baya a Najeriya, muka dinga komawa baya a cikin al’amura, wato sa kabilanci da bambancin addini a gaba, da ba shi tasirin da ba ya sa kyakkyawar soyayya da kyakkyawar mu’amala a tsakanin ’yan kasa.

Kasashen da a baya suke fama da irin wannan matsalar, a yau an wayi gari sun zama tamkar aljanna a duniya.

Ya ishe mu karamin misali, kasar Ruwanda, kasar da ta shiga matsanancin yanayi na rikicin kabilanci wanda ya hadu da na addini aka kashe rai kusan dubu 100 a shekara guda.

A yau Ruwanda ta zama kamar wata aljanna a duniya sakamakon jajirtattun shugabanni da suka samu masu kishi da burin ci gaban kasar ba wai wata kabila ko wani addini ba.

Don haka, ya kamata mu dangwala kuri’unmu ga ’yan takarar da ba za su cutar da wata kabila don faranta wa wata ba, ba za su cutar da wata akida don faranta wa wata ba, ba za su cutar da wani addini don faranta wa wani ba.

Wadanda za su tsaya tsayin daka wajen ceto kasarmu daga kassarewar tattalin arziki, wadanda za su tallafa wa matasan cikinta domin samar musu da gobe mai kyau, wadanda za su daidaita tsakanin talaka da mai kudi a kan dukan hakkokinsu.

Kada mu zabi wadanda za su dafa wa azzalumai wajen zaluntar raunana, kada mu zabi wadanda rayuka za su salwanta sakamakon sakacinsu ko kuma dafawarsu, kada mu zabi wadanda za su fifita akidarsu a kan maslahar al’umma.

Kada mu zabi wadanda ba su da isasshiyar lafiyar da za su gudanar da harkokin mulki.

Ranar zabe guda daya ce tal, kada mu yi kuskuren zabar wadanda ba su cancanta ba.

Idan kuwa muka yi kuskure muka zabi wadanda ba su cancanta ba, za mu samu koma-baya na tsawon shekara hudu sakamakon kuskuren rana dayar nan da muka yi.

Mu zabar wa kanmu da kasarmu ci gaba kada a rude mu da dan abin da bai taka kara ya karya ba.

Kowanenmu ya farka, ya yi kyakkyawan nazari da tunani a kan me zai faru da shi a tsawon shekara hudu idan ya dangwala wa wane kuri’arsa.

Shin biyan bukatar da za ka samu da ’yan dubban da za a ba ka, ka sayar da ’yancinka zai wadace ka na tsawon shekara hudu?

Shin za su taimaka maka idan ka je ko aka kai ka asibiti?

Za su ciyar da kai da iyalanka na tsawon shekara hudu?

Za su samar wa ’ya’yanka ilimi wadatacce?

Za su inganta rayuwarka da rayuwar wadanda suke karkashinka?

Za su samar maka da cikakken tsaro da aminci a gidanka?

Tuna makomar al’umma duka a hannunsa take, shin ci gaba zai zama ga kasarmu ko kuwa ci baya.

Ya zama dole mu muhimmanta wannan dama da muke da ita ta gyara Najeriya a cikin shekara hudu.

Masu iya magana suka ce, kowa ya yi da kyau, zai ga da kyau.

Don haka jama’a mu farka, mu zabar wa kanmu wadanda suka cancanta a wannan zabe na 2023.

A karshe muna yi wa kasarmu da al’ummarmu addu’ar Ubangiji Allah Ya ba mu shugabanni na gari, masu kaunarmu da son ci gaban kasarmu, amin.

Daga Mohammed Bala Garba da Aliyu Samba ke muku fatan alheri. 08098331260.