“Ni ne Hamisu Bala da aka fi sa ni da Wadume. ’Yan sanda sun zo Ibbi suka kama ni, suna tafe da ni ne lokacin da sojoji suka bi su suka kuma bude musu wuta, abin da ya yi sanadiyyar rasuwar wadansu ’yan sanda. Daga nan sojojin suka dauke ni zuwa hedkwatarsu, inda suka cire min ankwar da ke hannuna, kafin in tsere. Tun wancan lokacin nake buya har zuwa lokacin da aka sake kama ni.” Bayanin matashin nan ke nan wato Wadume da ake zargin kasurgumin mai garkuwa da mutane don neman kudin fansa da ya addabi mutane a wasu sassan Jihar Taraba da makwabtanta, a wani faifan bidiyo, bayan ’yan sanda sun sake kama shi a Kano ranar Litinin 19 ga Agustan nan.
A ranar 6 ga watan Agusta ne wani ayarin ’yan sanda da ke aiki a karkashin ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Alhaji Mohammed Adamu suka yi nasarar kama Wadume a garin Ibbi, mahaifarsa da ke Jihar Taraba, saboda koke-koken jama’a da suka yi ta samu kan yadda matashin da bai wuce shekara 31 ba, yake bushasha da kudaden da ba a san inda yake samunsu ba, kasancewar zuwa shekarar 2015, ba ya da komai, sai ma bangar siyasa da yake yi. Dadin dadawa kuma ba ya da tarihin ya gaji wata dukiya daga iyayensa ko ’yan uwa.
Amma bayan nasarar kama shi ne sai wadansu sojoji daga Bataliya ta 93 da ke garin Tukum a Jihar Taraba da ake zargi suna aiki bisa ga umarnin Kwamandan Ayyuka na Bataliyar, Kyaftin Tijjani Balarabe suka bi ’yan sandan, inda daga karshe suka kubutar da Wadume, kuma abin da ya gudana, ya gudana kamar yadda shi Wadume da kansa ya fadi a wancan faifan bidiyo. A sanadiyar kai wancan farmaki ne don ceto Wadume, sojojin suka kashe ’yan sanda uku da wani farar hula.
’Yan sandan da suka rasu sun hada da Sufeto Mark Edaile da Saje Usman Dan’azumi da Saje Dahiru Musa da kuma farar hula Mista Olajide Owolabi da kuma wadansu mutum shida da suka jikkata duk a harin kwato Wadume.
Aukuwar hakan ta sa aka yi ta cacar-baki a tsakanin sojoji da ’yan sanda, inda kowa ke fadin nasa bahasin.
Sojojin sun ce kiran neman dauki ko ceton rai suka samu, cewa wadansu masu garkuwa da mutane sun sace wani, shi ya sa suka kai farmakin. Ita kuma Rundunar ’Yan sanda ta Kasa ta musanta wancan ikirari na sojojin. Mai yiwuwa don ta ba da dama ga ’yan kasa su san wa ke karya a tsakaninta da sojojin, ya sanya bayan sake kama Wadume Rundunar ’Yan sandan ta sa shi ya yi wancan jawabi da ta nada kuma ta sakar wa duniya.
Saboda muhimmancin wadanda aka kashe da kuma a kan aikin da aka kashe sun da wadanda ake zargin sun yi kisan da abin da ake zargin ya sa suka yi kisan da cacar bakin da ta biyo bayan kisan a tsakanin manyan jami’an tsaron biyu, ya sa tun kafin a kai ga sake kama Wadume, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Babban Hafsan Tsaro da lallai ya binciki musabbin kisan wadancan ’yan sanda uku da farar hula. A gefe daya kuma rahotanni sun tabbatar da cewa Kyaftin Tijjani da sauran sojojin da ake zargin sun yi wancan aika-aika tuni suna can tsare a hannun sojojin.
Bari in dan waiwayi abin da ake zargin wala-alla shi ya sa sojojin a karkashin umarnin Kyaftin Tijjani Balarabe suka kai wancan farmaki don ceto Wadume da ake zargin kasurgumin mai yin garkuwa da mutane ne.
Da farko wasu jaridu da suka yi bincike a kan tarihin rayuwar Kyaftin Tijjani, sun tabbatar da cewa a Unguwar Tudun Fera da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jos babban birnin Jihar Filato ya taso, kuma a can ya yi karatunsa na firamare da sakandare, har lokacin da ya shiga aikin soja a matsayin kurtu a wajejen 1992 zuwa 1993. An ce mahaifinsa malamin addinin Musulunci ne dan asalin Jihar Kano, mahaifiyarsa kuma ’yar asalin Jihar Taraba ce. Wannan ya sa ake zargin Kyaftin Tijjani yana da dangantaka ta jini da Wadume, kodayake babu tabbacin wannan labari daga dangi.
Ko ma dai mece ce dangantakar Kyaftin Tijjani da Wadume, koda kuwa ciki daya suka fito, ka iya cewa Kyaftin Tijjani ya wuce makadi da rawa a kan rawar da ya taka a wajen kubutar da Wadume. Abin da wadansu suke zargin Kyaftin Tijjani ya yi haka ne don kudin da kawai yake samu daga Wadume.
Rahotanni kuma sun tabbatar da irin yadda Wadume ke yi wa mutanen yankinsa hidima manya da kanana, ’yan siyasa da masu mulki da manyan gari. Don an yi zargin cewa a zaben bana ya raba motoci da babura da suka kai 200 baya ga kudi da aka yi kiyasin sun kai Naira miliyan 100 ga wadansu ’yan siyasar jiharsa ta Taraba.
Wannan ya sa Wadume ba ya tabuwa a yankin duk da cece-kucen da mutanen yankin suke yi na zargin inda yake samun kudi.
Mai karatu abin la’akari a nan shi ne harkar Wadume, ita ce wadda ni da kai muka sani, na irin yadda mafi yawan mutanen wannan zamani muke girmama kudi fiye da mutunci.
Dubi irin yadda Wdume a zamansa na matashi ya samu goyon bayan mutane har da jami’an tsaro don kawai yana ba da kudi. Allah Ya sawwaka, Ya tsare mu da toshewar basira irin ta wannan zamani.
Saura da me? Tunda Wadume da mukarrabansa masu yi masa hidima ko ba shi kariya irin su Kyaftin Balarabe sun shiga hannu kuma rahotanni na cewa tunda aka kama Wadume aka samu sauki matuka na yin garkuwa da mutane a kusan dukkan jihar ta Taraba, yanzu babban aikin da ’yan kasa da ma duniya suka sa ido su gani bai wuce irin hukuncin da za a yi musu ba, musamman na irin rawar da su Kyaftin Tijjani suka taka, na kashe jami’an tsaro a bakin aikinsu, don kubutar da wanda ake zargin kasurgumin mai laifi ne. Ina fata wannan zai sa dukkan jami’an tsaron kasar nan su tashi tsaye wajen kakkabe batagarin da ke cikinsu irin su Kyaftin Tijjani da ake zargi koda kuwa ta zartar da hukuncin kisa ne.
Da ma tsohon Shugaban Kasa Dokta Goodluck Jonatahan (da ya yi wa annobar Boko Haram rikon sakainar kashi), ya sha zargin cewa a cikin jami’an gwamnatinsa akwai ’yan Boko Haram amma har ya bar mulki bai tona asirinsu ba, balle ya hukunta su. Lokaci ya wuce da za a rika yin haka.