✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sturridge ya sake jin rauni

Shahararren dan kwallon Ingila da kulob din Liberpool Daniel Sturridge a ranar Talatar da ta gabata ne ya sake jin rauni a lokacin da yake…

Shahararren dan kwallon Ingila da kulob din Liberpool Daniel Sturridge a ranar Talatar da ta gabata ne ya sake jin rauni a lokacin da yake yin atisaye da kulob din kwallon kafa na Ingila ana gab da yin wasan sada zumunta a tsakanin Ingila da Sukotlan.

dan shekara 25, ya yi nasarar zura wa kulob din Liberpool kwallaye 25 a bara, amma ya zuwa wannan lokaci wasa uku yayi wa kulob din a kakar wasa ta bana da hakan ya sa kulob din yake cikin matsala.
Hasalima a makon jiya ne ya fara yin atisaye a shirye-shiryen dawowarsa fagen daga a kulob din na Liberpool tun bayan ya samu rauni a watan Satumbar bana sai ga shi ya sake jin wani rauni a ranar Talatar da ta gabata.
Kulob din Liberpool dai yana cikin matsala don a kakar wasa ta bana ya samu nasara ne a wasanni hudu kacal daga cikin 14 da hakan ta sa yake matsayi na 11 a gasar rukunin firimiya na Ingila.