✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Stone ya koma City a kan Naira biliyan 23

Jone Stone dan kwallon baya a kulob din Eberton ya canza sheka zuwa kulob din Manchester City a kan Fam miliyan 47 da dubu 500…

Jone Stone dan kwallon baya a kulob din Eberton ya canza sheka zuwa kulob din Manchester City a kan Fam miliyan 47 da dubu 500 kwatankwacin Naira biliyan 23 da Miliyan 987 da dubu 500.
Stone, dan shekara 22 dan asalin Ingila ya rattaba hannu ne a kwantaragin shekara biyar kuma shi ne na 8 a jerin ’yan kwallon da sabon koci Pep Guardiola ya sayo wa kulob din Manchester City a bana.