✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sterling Bank zai raba kyautar katin cira kudi 100,000

Babban bankin kasuwanci a Najeriya, Sterling Bank zai raba kyautar kutunan cirar kudi guda 100,000 ga kwastomominsa a fadin kasar. Shugaban Sashen Huldar Bankin Zamani…

Babban bankin kasuwanci a Najeriya, Sterling Bank zai raba kyautar kutunan cirar kudi guda 100,000 ga kwastomominsa a fadin kasar.

Shugaban Sashen Huldar Bankin Zamani na Sterling Bank, Dipo Aladebe, ya ce masu asusun ajiya na Savings ko Current da ke amfani da sabon manhajar bankin na OneBank su ne suka cancanci samun kyautar.

Oladebe ya ce bankin zai kai wa wandanda suka bayyana bukatar katunan na Verve zuwa duk inda suka zaba kyauta ba sai sun wahala ba.

Yadda manhajar OneBank za ta sauya harkar banki a Najeriyar —Sterling Bank

Sterling banki ya gano damar harkokin kasuwanci iri-iri bayan wucewar COVID-19

“Banda kwastomomin da wa’adin katinsu bai kare ba a cikin masu cin gajiyar rabon kyautar katunan cirar kudin; a kokarin bankin na yaba wa abokan hulda da suka zabe mu a matsayin bankinsu”, inji sanarwar.

Ya ce ana bukatar masu son kyautar su yi amfani da OneBank akalla sau daya kafin su cancanci samun katin.

Ya ba da tabbacin cewa cikin ranakun aiki biyu zuwa biyar kwastomomi masu bukatar katunan za su samu a Legas.

Na sauran sassan Najeriya kuma za su samu cikin ranakuna aiki biyu zuwa bakwai.