Gwamnatin kasar Spain ta bai wa Najeriya gudunmawar rigakafin COVID-19 samfurin Johnson and Johnson guda miliyan hudu.
Jakadan Spain a Najeriya, Mista Juan Sell ne ya bayyana hakan sa’ilin da yake mika gudunmawar ga Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa (NPHCDA) a ranar Talata.
Jakadan ya ce, wannan ita ce gudunmawar rigakafin cutar mafi tsoka da kasarsa ta bai wa wata kasa a nahiyar Afirka.
Sell ya ce gudunmawar na mazaunin cika alkawarin da Gwamnatin Spain ta dauka ne na ninka kokarinta wajen tallafa wa kasashe masu tasowa a fagen yaki da annobar Kwarona.
Ya ce, “Daga 2020 zuwa 2021, duniya ta mai da hankali ne wajen kirkiro rigakafin Kwarona. Sannan a 2022, akwai bukatar a isar da maganin da aka samar din ga jama’a don su amfana.”
Ya kara da cewa, bukatar tabbatar da fasahar samar da rigakafin cutar ta karade ko ina musamman kasashen Afirka, hakan ya sanya kasar ta Spain hada kai da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) don cim ma bukatar hakan.
Daraktan NPHCDA, Dokta Faisal Shu’aib, shi ne ya karbi gudunmawar maganin a madadin Gwamnatin Najeriya, kana ya yi wa kasar godiya tare da cewa gudunmawar ta zo a daidai lokacin da ake da bukatar ta.