✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Son banza 2

Wani dan acaba ne yana yawo tsakar dare yana neman fasinja, yana cikin tafiya sai wani mutum ya tsaida shi. Yana rike da wata leda,…

Wani dan acaba ne yana yawo tsakar dare yana neman fasinja, yana cikin tafiya sai wani mutum ya tsaida shi. Yana rike da wata leda, yana hawan mashin din sai ya mika wa dan acabar nan ledar; ya ce ya rike masa. Da suka isa wurin da zai sauka, sai ya biya kudi ya yi tafiyarsa, ya manta da wannan leda da ya ba dan acaba riko. Shi kuma dan acaba ko da ganin haka sai kawai ya ruga da wannan leda, bai tsaya ko’ina ba sai gida. Yana zuwa ya ce wa matarsa: “dauko kwano.” Yana kwance leda sai ga kan kare da kafafuwa an babbake su. Matar ta dubi mijin ta ce: “Maigida wannan fa?” Sai ya ce: “Son banza ne ya kawo hakan.”

Daga Ashraf, 08152073868