Sojoji sun ceto mutum 13 da ’yan bindiga suka sace, suka kama wasu mutane 11 dauke da makamai a Jihar Zamfara.
Mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji, Kyaftin Yahaya Ibrahim, ya ce ranar Lahadi ne sojojin suka fara aikin bincike da ceto mutane a yankunan Gobirawan Chali da Dangulbi da Dansadau a Karamar Hukumar Maru ta jihar.
- Sarkin Ebira: Mutum 71 sun fito takarar kujerar Ohinoyi
- Yadda Za Ku Gane Kayan Abinci Marasa Inganci Nan Take
Ya ce dakarun suka ceto mutum 13 da ’yan ta’adda suka sace a ranar daga kauyen Mutunji a karamar Hukumar.
“Duk wadanda aka ceto an mika su ga wWakilin Gwamnatin Jihar Zamfara don hada su da iyalansu.”
Sanarwar ta ce, “Rundunar ta gano maboyar ’yan ta’adda a Gidan Jaja a Karamar Hukumar Zurmi.”
Ya kara da cewa sojojin sun kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne 11 wadanda ke ba da kayan aiki ga wani fitaccen dan ta’adda Halilu Sububu a Kwanar Boko a Karamar Hukumar Zurmi.
“An kama wadanda ake zargin ne lokacin da suke dauke da buhunan hatsi 127 a cikin manyan motoci 2 na dan ta’adda Halilu Sububu. Amma a yanzu haka, ana bincike a kan su.”