Rundunar sojojin sama sun ce sun yi imanin matar shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, Malama Fiddausi ta mutu a wani harin sama da jiragen saman sojojin suka kai a maboyarsu a kauyen Durwawa.
Durwawa kauye ne da ke cikin karamar hukumar Konduga da ke cikin jihar Borno.
Daraktan yada labarai na rundunar sojojin saman, Iya Kwamanda Olatokunbo Adesanya ne ya tabbatar da kisan.