Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta ce ta gano wani bututu da aka kafa a jikin wata rijiyar hakar danyen man fetur da ake amfani shi wajen satar man a Jihar Ribas.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa rijiyar da aka gano bututun a jiki mallakin Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ce mai lamba 18.
- Tsawa ta kashe masu garkuwa da mutane su 3 a Kwara
- Tinubu na son majalisa ta sahale masa kashe biliyan 500 na rage radadin cire tallafi
Kwamandan wani jirgin ruwan rundunar mai suna Pathfinder, Sulaiman Ibrahim, ne dai ya zagaya da manema labarai a wajen da aka gano bututun a gundumar Kala Ekweama da ke Karamar Hukumar Asari-Toru ta Jihar.
Kwamandan ya ce, “Wani jirginmu mai saukar angulu ne ya gano wajen yayin wani sintirin da ya saba yi a hanyoyin ruwa da gabobin teku na yankin.
“Jima kadan da gano haka, sai muka girke jiragenmu na ruwa a wajen muka kuma fara sanya idanu, sannan mu tabbatar da an kawo karshen wannan haramtaccen aikin da ake yi.
“Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya tana yin duk mai yiwuwa wajen kakkabe ayyukan barayin mai a yankin Neja Delta,” in ji shi.
Suleiman ya ce wasu daga cikin abubuwan da suka kama a wajen sun hada da kwalekwale da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen satar man daga kan rijiyar.
“Mun tuntubi masu kula da rijiyar kan su aike da kwararrun ma’aikatansu su duba wajen, amma suka ce an yi matukar yin ta’adi a wajen,” i ji shi.
(NAN)