Rundunar Sojojin Najeria ta ce kera manyan jiragen yakin ruwa guda hudu a yunkurin ta na kawo karshen matsalar satar mai da fashin teku a yankin na Neja Delta.
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Leo Irabor ne ya tabbatar da haka a birnin Fatakwal na Jihar Ribas ranar Talata.
- Yadda Liverpool ta yi wa Manchester United wankin babban bargo
- Jihar Kano neman karin kaso na musamman daga kudaden Gwanatin Tarayya
Yana jawabin ne a wajen kaddamar da jiragen ruwan a babbar tashar jiragen ruwa da ke Fatakwal.
A cewar Janar Irabor, sabbin jiragen da kamfanin Naval Shipyard Limited (NSL) da ke Fatakwal ya kera, za su kara samar da kariyar da ake bukata ga sojojin da ke sintiri a gabar tekun domin dakile barazanar ciki da waje.
Ya kara da cewa, yankin tekun Najeriya yanki ne da ke da albarkatun kasa, ciki har da mai da iskar gas, don haka ya wani babban jigon tattalin arziki ne ga kasar.
“Saboda haka, kare wadannan albarkatun shi ne babban abin da Gwamnatin Tarayya ta mayar da hankali don dorewar harkokin tattalin arziki da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na Neja Delta,” inji Janar Irabor.