✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sojojin Amurka sun kashe shugaban ISIS Abu Ibrahim a Syria

Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi ne ya karbi ragamar ISIS kwanaki kadan da mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi.

Wasu sojojin Amurka na musamman sun kashe shugaban kungiyar ISIS, a wani samame da suka kai cikin dare a lardin Idlib da ke Arewa maso Yammacin Syria.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Fadar White House ranar Alhamis.

“A daren jiya bisa umarnin da na bayar, sojojin Amurka sun samu nasarar gudanar da wani aiki na yaki da ta’addanci a Arewa maso Yammacin Syria domin kare alummar Amurka da wadanda muke kawance da su sannan kuma mu tabbatar da amince a wannan duniya da muke rayuwa,” a cewar Shugaba Biden.

An kai harin ne kan Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi, wanda ya karbi ragamar shugabancin kungiyar a ranar 31 ga Oktoban 2019, kwanaki kadan bayan mutuwar shugaba Abu Bakr al-Baghdadi a wani farmaki da Amurka ta kai a yankin.

Wannan farmakin ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar ISIS ke kokarin sake bullowa, tare da kai wasu hare-hare a yankin, ciki har da harin kwanaki 10 a karshen watan da ya gabata na kwace wani gidan yari.

Dakarun Amurka na musamman sun sauka na a cikin jirage masu saukar ungulu tare da kai farmaki a wani gida a wani yanki da ke hannun ’yan tawaye a Syria, inda suka shafe sa’o’i biyu suna artabu da ’yan bindiga, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Kamfanin Dillancin Labarai na AP (The Assocciated Press) ya ruwaito cewa, uwar bari ce ta sanya shugaban na ISIS ya tayar da wani bom wanda ya yi ajalinsa da na iyalansa yayin da dakarun Amurka suka ritsa shi a gida.

Mazauna yankin sun bayyana ci gaba da harbe-harbe da fashe-fashe da aka yi a garin na Atmeh da ke kusa da kan iyakar Turkiyya, yankin da ke da sansanonin ’yan gudun hijira daga yakin basasar Siriya.

Masu ba da bayani na farko sun ce an kashe akalla mutane 13 da suka hada da yara shida da mata hudu kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.